A ranar Litinin din da ta gabata 1 ga watan Augusta shekara ta 2022 a ka gudanar da addi’oi na musamman a kananan hukumomin Funtuwa da dandume da Bakori da Danja da karamar hukumar Sabuwa dake Jihar Katsina domin samun zaman lafiya ganin yadda sha’anin tsaro ya tabarbare a yankin da yadda ‘yantadda ke cin karensu babu babbaka a yankin dama sauran sassan jihar.
Addu’ar ta sami halartar manyan malaman izala da darika na dukkan kananan hukumomin yankin addu’ar wadda ake kira da (Yaumal shukur) wadda ake gabatarwa duk shekara an gudanar da karatun Alkur’ani maigirma da sauran addi’oi tun da misalin karfe 10 ma safiyar ranar aka fara gudanar da addioin a dukkan dakunan taro na kananan hukumomin.
- Wasu Nau’in Kwadi Da Macizai Sun Haddasa Asarar Dala Biliyan 16 A Duniya
- Amurka Ce Ke Yi Wa Zaman Lafiya A Zirin Taiwan Barazana
Dukkan shugabannin kananan hukumomin tare da hakimansu da kansilolin kananan hukumomin suka halarta.
A lokacin da suke nuna jin dadinsu da kuma godiya ta musamman ga maigirma Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Bello Masari, shugabannin kananan hukumomin na Funtuwa Malam Lawal Sani Matazu wanda sakataren karamar hukumar Malam Salihu Danladi ya wakilta tare da hakimin Funtuwa Sarkin Maskan Katsina Alhaji Sambo idris Sambo da sauran manyan jami’an karamar hukumar da shugaban karamar hukumar Bakori Alhaji Ali Maicitta da hakimin Bakori Alhaji Idris Sule Idris dana Danja Alhaji Rabo Tambaya Danja da hakimin Danja Sarkin kudu Alhaji Bature da shugaban karamar hukumar dandume Alhaji Ya’u Nowa da takwaransa na karamar hukumar Sabuwa Alhaji Faruku Hayatu da Kogon Katsina hakimin Sabuwa Injiniya Bello Ibrahim sun yaba wa dukkan malaman yankin da sauran jama’ar yankin ganin yadda suka tashi tsaye wajen gudanar da irin wadannan addi’oin domin samun zaman lafiya.