Kwararru a harkar kimiyya da ke tattara asarar da wasu mugayen kwari suka haifar a fadin duniya sun gano wasu halittu biyu da suka jawo asara fiye da sauran.
Nau’in kwado dan Amurka da ake kira American bullfrog a Turance da kuma jan maciji – da ake kira brown tree snake a Turance, sun haddasa asarar kudin da suka kai Dala biliyan 16 da 300,000, kwatankwacin Naira tiriliyan shida a fadin duniya tun daga shekarar 1986.
- Nijeriya Ta Yi Barazanar Ficewa Daga Kungiyar ECOWAS
- Wang Yi Ya Yi Cikakken Bayani Kan Matsayar Sin Game Da Yankin Taiwan
kari a kan albarkatun tsirrai da suka lalata, mugayen dabbobin sun kuma lalata amfanin gona sannan suka haifar da katsewar wutar lantarki.
Masu bincike na fatan abin da suka gano zai taimaka wajen tara kudade don dakile ayyukan mugayen dabbobi a nan gaba.
Cikin rahoton binciken da suka wallafa, masana kimiyya sun dora wa jan macijin alhakin haifar da barnar Dala biliyan 10.3 jimilla, ta hanyar karade wasu tsibirai a yankin Pacific.
A yankin Guam, inda sojojin Amurka suka kaddamar da macijin a karnin da ya gabata, ‘ya’yan nau’insa sun haddasa daukewar wutar lantarki da yawa saboda suna makalkalewa kan wayoyin lantarki tare da haddasa asara mai yawan gaske.
Akwai nau’in wannan maciji kusan akalla miliyan biyu a dan karamin tsibirin, inda wasu alkaluman ke cewa akwai akalla guda 20 a tsawon kowace girman eka na dajin Guam.
Ana ganin dazukan da ke tsibirai sun fi fuskantar hatsarin muggan dabbobi, inda suke yawan saka sauran dabbobin da ke rayuwa a wurin cikin hadarin karewa a bankasa.
A nahiyar Turai, akwai dandazon kwadi da ke bukatar a kula da su da kyau.
Don dakile hadarin kwadin, wadanda kan yi tsawon da ya kai na kusan kafa daya da kuma nauyin rabin kilo, sun tilasta wa hukumomi dasa shingaye a wuraren kiwo.
Saka shinge a wuaren kiwo biyar kawai don hana kwadin guduwa ya jawo wa hukumomin Jamus kashe kudi Yuro 270,000, kwatankwacin Naira miliyan 114, kamar yadda wani tsohon bincike na Tarayyar Turai ya bayyana.
Rahotanni na cewa dabbar na cin kusan komai, ciki har da ‘yan uwansa kwadi.
Ana zargin wani nau’in na kwado da aka fi sani da haddasa asara ta wata hanyar daban: karar kukansu ta sa darajar gidajen da ke kusa da su ta karye.
Masu bincike na fatan sakamakon abin da suka gano zai karfafa wa hukumomi gwiwa wajen samar da kudaden dakile barazanar dabbobi mugaye.