Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewar gwamnatin jihar za ta sauya wa makarantu 359 da ke wuraren da ake fama da matsalar tsaro matsuguni a jihar.
A ranar 7 ga watan Maris ne, ‘yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai sama da 250 daga makarantar firamare da ke garin Kuriga, daga bisani maharan suka sako dalibai 167 makonni biyu bayan wani hari da sojoji suka kai musu.
- Kwastam ta Mika Jabun Dalar Amurka Da Jirage Marasa Matuka 148 Da Ta Kwace Ga EFCC Da Sojoji
- An Gabatar Da Shirin Talabijin Mai Suna Labarun Da Xi Jinping Ya Fi So A Hungary
Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar, Sani Kila ne, ya bayyana matakin yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a jihar.
Matakin, wani bangare ne na shirin gwamnatin tarayya na kare makarantu, wanda ke da nufin inganta matakan tsaro don kare cibiyoyin ilimi, dalibai da malamai daga hare-haren ‘yan bindiga.
Da yake bayyana damuwarsa kan yadda masu hannu da shuni ke kawo cikas ga harkokin tattalin arziki da zamantakewa, Gwamna Sani ya jaddada muhimmancin da ke tattare da kare fannin ilimi a jihar.
Ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun raguwar daliban da ke shiga makarantu a jihar, inda akalla daliban Firamare sama da 200,000 suka daina zuwa makaranta a zangon karatu na shekarar 2022/2023.
Gwamna Sani ya danganta koma bayan da aka samu da rashin tsaro musamman a yankunan Chikun da Birnin Gwari da Kajuru da Giwa da kuma Igabi, inda matsalar tsaro ta fi kamari.
“Domin samar da ilimi ga yaran da ke zaune a yankunan da ake fama da matsalar tsaro, gwamnati ta fara shirin sauya wa makarantu 359 matsuguni saboda tsaro,” in ji Gwamna Sani.