Ana samun karuwar tashin hankali a jihohin arewa maso yammacin Nijeriya, musamman a jihohin Kaduna, Zamfara, Kebbi, da Sakkwato, wanda ya sanya gwamnonin jihohin lalubo dabarbarun dakile garkuwa da mutane da farfado da zaman lafiya a jihohin nasu.
Wadannan dabarbarun da suka kunshi tattaunawar sulhu ko kin amincewa da shi, an gano ra’ayoyi daban-daban da ke nuna irin yadda ake samun rashin hadin kai a tsakanin shugabannin arewa wajen magance matsalar tsaro.
- Yadda Jami’an Tsaro Suka Fara Gyara Wa ‘Yan Jari Bola Zama A Abuja…
- Babban Jami’in JKS Ya Yi Kira Da A Ci Gaba Da Kawar Da Ayyuka Mara Ma’ana
Ko a ‘yan kwanakin nan, gwamnonin jihohin da lamarin ya shafa sun yi ta kokarin nemo wasu hanyoyin kawo karshen matsalar tare da ra’ayoyin kwararrun masana harkokin tsaro kan lamarin.
Gwamnonin masu ra’ayoyi daban-daban kan matsalar tsaro na ba da hujja da abun da gwamnatinsu take ganin su ne mafita da kuma kokarin da suke yi na ganin sun kare jama’ansu.
A Kaduna, Gwamna Uba Sani ya kare shirin gwamnatinsa na yin sulhu da zaman lafiya da ‘yan bindiga da suke addabar jama’a a wasu sassan jihar.
Ya ce, aikin farko da ke kan kowace gwamnati shi ne kare rayukan da dukiyar jama’a tare da tabbatar da zaman lafiya. Don haka ne ya yi cikakken bayani kan shirin sulhun da aka kwashe sama da watanni shida ana yi da masu garkuwa da mutane kuma sulhun ba ta hada da bayar da ko sisi ga ‘yan bindigan ba.
Ya ce, “Ba mu ba su ko sisin kwabo ba. Ko naira daya ba mu ba su ba. Babban abun da muka sanya a gaba shi ne kare al’ummarmu da tabbatar da zaman lafiya a jihar.”
Shirin ya haifar da sakamakon mai matukar kyau. A ranar 29 ga watan Nuwamban 2024, ya amshi ‘yan bindiga dadin da suka tuba a Birnin Gwari tare da sake bude kasuwar shanu da aka rufe tsawon shekaru sakamakon matsalar rashin tsaro.
Gwamnan ya shaida cewa manya-manyan shugabannin ‘yan bindiga da dama tare da magoya bayansu sun ajiye makamai tare da rungumar zaman lafiya.
Gwamnan ya ce da ran mutum guda ya salwanta gara ya yi komai domin kare al’ummar jihar, saboda shi ne Allah zai tambaya a ranar kiyama kan yadda ake kashe rayuka a lokacin da yake mulkin jihar.
A Jihar Zamfara kuwa, sauyin gwamnati na daga cikin dalilan da suka shafi magance matsalolin tsaro a jihar.
Tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya yi ta kokarin sulhu da ‘yan fashin dajin da nufin kawo karshen garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
Ya hakikance kan cewa sulhun ita ce hanya mafi sauki na yaki da ‘yan fashin daji kuma a ta irin wannan sulhun ya samu nasara har aka saki ‘yan mata 26. Amma, gwamnatinsa ba ta samu zarcewa ba balle ta kara shirin da ta faro.
Sai dai kuma, gwamnati mai ci a halin yanzu ta Gwamna Dauda Lawal, ta kage kai da fata cewa atafaf babu wani zancen sulhu da ‘yan fashin daji.
Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta shiga wani sulhu da ‘yan bindiga da suke ta’addanci a jihar ba.
Gwamnan ya ce, “Har yanzu muna kan matsayarmu cewa ba za mu yi sulhu da ‘yan ta’adda ba. Gwamnatinmu ba ta da shakka ko kadan kan matakan da muke dauka wajen shawo kan matsalar tsaro da jiharmu ke fama da shi.”
A baya dai, hanyar Abuja zuwa Kaduna ya zama wani hanyar garkuwa da mutane bisa yadda masu sace mutane ke cin karensu babu babbaka, lamarin da ke jefa razani a zukatan matafiya a kowani lokaci. Amma a yanzu hanyar ta yi lafiya wanda aka dade ba a ji lamarin sace wani mutum daya ba.