Majalisar Wakilai ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya kirkiro sabon shiri domin kawo karshen kisan kai, satar mutane, da sauran ayyukan fashi da makami a Jihar Zamfara da kasar baki daya.
Wannan kira ya biyo bayan amincewa da tayin gaggawa na al’ummar kasa da dan majalisar da ke wakiltar Gusau/Tsafe Federal Constituency na Jihar Zamfara, Hon. Kabiru Amadu, ya gabatar a zaman majalisa ranar Talata.
- Li Qian: Ya Kamata A Aiwatar Da Sakamakon Taron Kolin Tianjin Don Inganta Kungiyar SCO
- Gwamnan Kano Ya Ɗauki Malaman Lissafi 400 Aiki
A yayin gabatar da tayin, Amadu ya bayyana cewa la’akari da matsalolin tsaro marasa iyaka a Jihar Zamfara da kasar baki daya, ya dace a ce “gwamnati ta yi isasshen aiki wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya domin su gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.”
Ya bayyana cewa ’yan bindiga masu makamai masu karfi sun kai farmaki wasu sassan Jihar Zamfara inda suka kashe mutum sama da 10, sace mutane 130, sannan suka dora haraji mai yawa har Naira miliyan 100 ga wadannan al’ummomi masu rauni.
Amadu ya ce ’yan bindigan suna gudanar da laifukansu ne ta hanyar hawa babura, inda ba za ka rasa kasa da mutum biyu zuwa uku a kowane babur ba, suna zagayawa daga wani yanki zuwa wani tsawon makonni biyu zuwa uku, dauke da makamai ba tare da wani kalubale mai inganci daga hukumomin tsaro ba.
Ya nuna damuwarsa cewa, “Bukatar biyan Naira miliyan 100 a haraji ba dai-dai ba ne kuma ba mai yiwuwa ba ne ga jama’a da suka riga sun sha wahala saboda rasa rayuka da dukiyoyi, inda manyan ayyukan tattalin arzikinsu noma ce da kananan sana’o’i, wadanda duk sun sami matukar illa saboda tashin hankali da ke ci gaba da matsawa al’ummomin cikin talauci da damuwa mai zurfi.”
“Wannan rikici ya haifar da mawuyacin yanayin jin kai, inda mazauna ke rasa abubuwan bukatu na yau da kullum kamar abinci, kiwon lafiya da tsaro; tsoro yana mamaye su yayin da al’ummomi ke rayuwa karkashin barazanar sake kai farmaki da bukatar kudin fansa.
“Wannan kisan da aka ambata su kadai misalai ne daga cikin tarin kisan kai da satar mutane da suka faru a cikin wata guda kacal a mazabar da nake wakilta,” in ji shi yana nuna damuwa.














