A kokarinsa na magance matsalar tsaro, Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya kai ziyara kwana biyar Jihar Zamfara, inda zai zaga garuruwan da matsalar tsaro ta addaba.
Da yake magana a gidansa da ke Gusau yayin taron magoya bayan jam’iyyar APC, Matawalle ya bayyana cewa wannan ziyara ta aiki ce kamar irin wadda ya kai Jihar Sakkwato kwanan nan.
- Kirsimeti: NSCDC Za Ta Jibge Jami’ai 3,542 A Kano
- An Bude Sabon Babi A Yankin Macao Wajen Aiwatar Da Manufar Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu A Cikin Shekaru 25
Ya ce ziyarar na da nufin gano matsalolin tsaro kai tsaye da kuma kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda da suka addabi jihar.
Matawalle ya kara da cewa wannan yunkuri yana daga cikin kudirin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na samar da jiragen yaki na zamani da makamai domin kawo karshen matsalar ‘yan bindiga kafin shekarar 2025.
Haka kuma, ya gargadi duk wanda ke taimaka wa ‘yan bindiga a cikin daji ko gari cewa hukuma za ta dauki mataki mai tsanani a kansu.
A karshe, Matawalle ya yi kira ga al’umma da su bayar da rahotanni na sirri ga jami’an tsaro domin taimakawa wajen cimma nasarar yakin da ake yi da ‘yan bindiga.