Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta kasa, NCC ta sake nanata umarnin da ta baiwa kamfanonin sadarwar da ke aiki a Nijeriya cewa, su tabbatar sun rufe duk layukan wayar da ba a haɗa su da lambar katin ɗan ƙasa ta NIN ba kafin wa’adin da aka gindaya musu.
Daraktan hulda da jama’a da yaɗa labaran hukumar, Mista Reuben Mouka ne ya bayyana umarnin a lokacin wani taron kasuwanci da aka gudanar a Kaduna, kamar yadda BBC Hausa ta rahoto.
- Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Takwaransa Na Saliyo
- Dole Ne Amurka Ta Daina Tsoma Baki Cikin Harkokin Gidan Sin Ta Fakewa Da Batun Hakkin Bil Adama
Mouka ya ce, an ɗauki matakin ne don magance matsalar tsaro da ke barazana ga ƙasar.
Mista Mouka ya jaddada wa’adin yau Laraba, 28 ga watan Fabrairu da aka bai wa kamfanonin sadarwar su rufe duka layukan da ba a haɗa da lambar NIN ba.
In ba a manta ba, hukumar NCC ta ɗaɗe tana kiran al’ummar Nijeriya da su haɗa lambar wayarsu da ta katin ɗan ƙasarsu (NIN) domin shawo kan kalubalen rashin tsaro a Nijeriya.