Wasu kamfanonin rarraba wutar lantarki a Nijeriya sun ce sun fuskanci matsala a yau Juma’a, lamarin da ya jefa wasu sassa na cikin duhu.
Kamfanin wutar lantarki na KEDCO, wanda ke bai wa Kano da makwabtanta wuta, ya nemi afuwar kwastomominsa.
- Gwamnati Ta Amince Da Bai Wa Jami’o’i 11 Masu Zaman Kansu Lasisi
- Masana Kimiyya Na Sin Sun Gano Tsare-Tsaren Rayuwa A Muhallin Halittu Mafi Zurfi A Teku
“Muna baƙin cikin sanar da ku cewa an samu matsala a layin lantarki da misalin ƙarfe 2 na rana, wanda ya hana mu bai wa kwastomominmu wuta,” in ji kamfanin a shafukan sada zumunta.
Shi ma kamfanin Ikeja Electric, wanda ke bai wa Legas da maƙwabtanta wuta, ya fitar da irin wannan sanarwa.
Sai dai, dukkaninsu ba su bayyana ainihin matsalar ba, kuma ba su danganta ta da matsalar babban layin lantarki na ƙasa ba.
Sau da yawa irin wannan matsala na faruwa idan layin wuta na ƙasa ya samu matsala.
Amma har yanzu, hukumar kula da rarraba wutar lantarki ta ƙasa Transmission Company of Nigeria (TCN), ba ta ce komai ba kan lamarin ba.
Matsalar ta shafi wurare da dama, ciki har da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp