Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta jaddada cewa, matsayin kasar na adawa da matakin Japan na zuba ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku, a bayyane yake kuma bai sauya ba.
Kakakin ma’aikatar ya bayyana haka ne jiya, yayin da yake tsokaci game da sanarwar Japan ta fara zagaye na biyu na zuba gurbataccen ruwan dagwalon tashar nukiliya ta Fukushima a cikin teku.
- Shawarar Kasar Sin Ta Gina Al’ummar Duniya Mai Mokamar Bai Daya
- Tsige McCarthy Daga Mukaminsa Ya Nuna Me Ake Nufi Da “Dimokradiyyar Amurka”
Kamfanin samar da makamashin lantarki na Tokyo wato (TEPCO) ya sanar a jiya Alhamis cewa, zai fara zagaye na biyu na zuba gurbataccen ruwan dagwalon da yawansa ya kai ton 7,800 a cikin teku, cikin tsawon kwanaki 17.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin ya kara da cewa, teku mallakin daukacin bil adama ne, kuma ya kamata gwamnatin Japan ta saurarai korafin al’ummun kasa da kasa, ta kuma tuntubi kasashe makwabtanta bisa gaskiya, kana ta zubar da gurbataccen ruwan dagwalon nukiliyar ta hanyar da ta dace. (Fa’iza Mustapha)