Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Yayin da yake magana game da matsayin Sin a kan harkokin tattalin arziki, ya ce, bangaren Sin na tsayawa tsayin daka kan goyon bayan dunkulewar tattalin arzikin duniya, da kuma inganta buda kofar tattalin arzikinta ga duniya.
- An Kafa Fiye Da Kamfanonin Waje 24,000 A Sin Cikin Watanni 5 Na Farkon Bana
- Ambaliyar Ruwan Mokwa: Masana Sun Shawarci Gwamnati Kan Matakin Kariya A Nan Gaba
Game da batun yadda wasu hukumomin hada-hadar kudi na kasa da kasa suka kara daga matsayin hasashen habakar tattalin arzikin Sin a kwanan nan kuwa, Guo Jiakun ya ce, a bisa yanayin da ake ciki na kasa da kasa mai sarkakiya, tattalin arzikin Sin yana bunkasa duk da matsin lamba, wanda hakan ya sa ya zama ginshiki mai kwanciyar hankali wajen ingnata tattalin arziki na duniya.
Game da batun yankin Taiwan na Sin, ya ce, bangaren Sin na mutunta hakkin zirga-zirgar jiragen ruwan dukkan kasashen dake mashigin tekun Taiwan bisa doka, amma tana matukar adawa da duk wata kasa dake tsokana bisa hujjar ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma barazana ga ikon mulkin kasar Sin. Ban da wannan kuma, “amfani da karfi wajen neman ‘yancin kai” da mahukuntan yankin Taiwan ke yi ba zai yi nasara ba.
Dangane da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, Guo Jiakun ya ce nuna karfi ba hanya ce da ta dace da warware rikicin kasa da kasa ba, kuma babban abin da ake bukata shi ne a hada kai don karfafa tsagaita bude wuta da kuma dakatar da yakin.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp