Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa al’ummar kasar nan kukan dadi suke yi idan aka kwatanta irin matsi da wahalar da ake sha a ragowar kasashen Afirka.
Shugaban yayi wannan jawabi ne a fadar Sarkin Katsina, Dakta Abdulmumini Kabir Usman, lokacin da ya je gaisuwar sallah a yau Asabar bayan gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, da Sarkin Katsina sun yi masa korafin irin wahalar da mutane suke sha a mulkinsa.
- Kano Ke Kan Gaba Wajen Shan Maltina, In Ji Kabiru Kasim
- El-rufai Ya Amince Da Daukar Karin Malamai 10,000
“Idan mutane suka san irin halin matsin rayuwa da wasu kasashen Afirka suke ciki a halin yanzu, dole su gode wa Allah game da halin da suke ciki a kasar nan.
Ya kara da cewa “Saboda haka muna kira ga mutane da su yawaita hakuri, muna iya bakin kokarinmu”
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yi wa Buhari addu’a domin mulkar al’umma irin ta Nijeriya mai kabilu da addinai da yawa na da wahalar gaske.
Tuni dai shugaban kasa ya koma babban birnin tarayya Abuja bayan kammala hutun sallah.