Jirgin sama mai saukar ungulu FT7-NI mallakin dakarun rundunar sojin Saman Nijeriya ya yi hatsari a Makurdi babban birnin jihar Benue.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a gano cikakken musabbabin faruwar hatsarin ba.
- Gwamnan Sakkwato Ya Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Tambuwal
- Musabbabin Haramta Sana’ar Gwangwan A Jihar Borno
Majiyoyi sun tabbatar wa LEADERSHIP cewa matukan Jirgin NAF su 2 da suke cikin Jirgin a lokacin da ta yi hatsari sun kubuta.
Shi ma Kakakin rundunar sojin Saman Nijeriya, Air Commodore, Edward Gabkwet ya tabbatar da labarin tare da cewa, FT-7NI jirgi ne na horaswa.
Ya ce Jirgin ya gamu da hatsarin ne wajajen karfe 4.15 na ranar Juma’a yayin da ke kan aikinsa da ya saba na horaswa.
“Bisa taimakon Allah matukan da ke ciki su biyu duk sun tsira. Kari a kan hakan babu asarar rayuka ko wani barnar da aka samu na kadarori a yankin da lamarin ya faru.
“Dukkanin matukan Jirgin a halin yanzu su na kan samun kulawar Likitoci a asibitin NAF da ke Makurdi.”
Kakakin ya sanar da cewa Shugaban sojin Sama, Air Vice Marshal Hasan Abubakar, ya kafa kwamitin da zai bincike musabbabin faruwar hatsarin Jirgin.