A wani shiri na neman mafita kan kalubalen da ‘yan Nijeriya ke fuskanta, babbar daraktar kungiyar cinikayya ta duniya (WTO), Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, ta yi wani hobbasa na hadin guiwa da shugaban kasa, Bola Tinubu domin lalubo mafita.
Dakta Okonjo-Iweala, a wata zantawa da ta yi da manema labarai jim kadan bayan ganawa da Shugaba Tinubu a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Talata, ta bayyana jin dadin ta da damar da ta samu na ganawa da shugaba Tinubu.
Dakata Ngozi ta samu rakiyar Dakta Muhammad Ali Pate, mai jiran mukamin Minista.
Ziyarar ta yi ta ne domin lalubo hanyoyin da za a iya bi wajen ba wa ‘yan Nijeriya tallafi kan wannan mawuyacin lokaci da suke ciki.
Ta bayyana matukar bukatar bayar da tallafi ga ‘yan Nijeriya a wannan mawuyacin lokaci.
Da take bayyana rawar da WTO ta taka, Okonjo-Iweala ta ce, WTO tana gudanar da shirye-shirye wanda za ta taimaka wa Mata ‘Yan Kasuwa musamman masu kanana da matsakaitan masana’antu a Nijeriya.