Gwamnatin Jihar Borno, ta ce akalla mayakan Boko Haram sama da 200,000 ne suka ajiye makamansu tun bayan kaddamar da shirin yjn afuwa a jihar.
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Baba Sheikh ya shaida wa manema labarai wannan nasarar da suka samu a ziyarar aikin da ya kai Legas.
- Shagulgulan Karamar Sallah: Me Aka Shirya Da Zai Bambanta Bara Da Bana?
- Jakadan Sin A Amurka: Sabon Karfin Samar Da Hajoji Da Hidimomi Masu Karko Ya Inganta Ci Gaban Sin Da Duniya
Ya ce gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ya gayyaci duk masu ruwa da tsaki a Borno domin tattauna yadda za a kaddamar da shirin bai wa mayakan damar dawowa cikin al’umma.
Ya ce bayan samun amincewar shugabannin al’ummomin jihar, gwamnati ta kaddamar da shirin na kwance damara da sauya tunanin mayakan da kuma sake mayar da su cikin al’umma.
A cewarsa tuni ya shirin ya samu karbuwa da kuma goyon bayan Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres wanda ya ziyarci jihar.
Sheikh ya ce a karkashin wannan shirin, gwamnatin jihar ta samar da waje, inda ta ke karbar tubabbun da kuma horar da su wajen sauya musu tunani.
Sheikh ya kuma bayyana cewar, sabanin yadda wasu jama’a ke tunani, ya zuwa wannan lokaci babu wata karamar hukuma a jihar da ke karkashin masu tada kayar baya.
Ya kara da cewa, wannan nasarar ce ta bada damar mayar da dubban ‘yan gudun hijira zuwa garuruwansu, bayan sake gina musu gidaje da cibiyoyin kula da lafiya da kuma kayan more rayuwa.