Mambobin kungiyar ‘yan tawaye tara dake neman a sako hambararren shugaban kasar Nijar sun mika wuya, kamar yadda jami’an kasar da sojoji ke mulka suka bayyana.
An kafa kungiyar ‘yan tawayen Patriotic Liberation Front (FPL) a watan Agustan shekarar 2023, wata guda bayan hambarar da zababben shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum a wani juyin mulki da sojoji suka yi.
- Zaɓen Ƙananan Hukumomi: PDP Ta Lashe Dukkanin Kujerun Shugabanni A Zamfara
- Manomanmu Sun Tabka Asarar Sama Da Naira Miliyan 100 A Harin ‘Yan Bindiga – Dan Majalisa
Tun a wancan lokaci Bazoum na tsare da matarsa Hadiza a fadar shugaban kasa da ke Yamai babban birnin kasar.
Gwamnan Agadez, wani jami’in yankin hamadar Arewacin kasar dake kusa da kasar Libya ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, mayakan FPL tara sun tuba tare da mika makamansu da alburusai a yayin wani biki a gaban Janar Ibra Boulama.
Mambobin FPL sun fara mika wuya ne a farkon wannan wata bayan tattaunawa mai ma’ana da wasu masu fada aji na kasar, kamar yadda kafar yada labarai ta Air-Info ta ruwaito.
A ranar 1 ga watan Nuwamba mai magana da yawun FPL Idrissa Madaki tare da wasu mambobi uku sun mika kansu a lokuta daban-daban a wasu garuruwa biyu da ke kusa da kan iyakar kasar Libya, kamar yadda sojojin Nijar da gidan talabijin na kasar suka bayyana.
A makon da ya gabata, an cire wa shugaban FPL Mahmoud Sallah, da kuma wasu mutane bakwai na gwamnatin Bazoum da ake zargi da kai hare-haren ta’addanci. ‘yancin zama ‘yan kasa na dan lokaci.
Sallah ya dauki alhakin kai hare-hare kan sojoji a Arewa da kuma lalata wani muhimmin bututun mai da ke dauke da danyen mai zuwa Benin a watan Yuni. Ya kuma yi barazanar kai hari a wurare masu mahimmanci.
Wata kungiyar ‘yan tawayen da ita ma ta ke neman a sako Bazoum, da ake kira, “Patriotic Front for Justice” (FPJ), tana tsare babban jami’in hukumar soji ta yankin Arewa maso Gabashin Bilma da wasu jami’an tsaronsa hudu, wadanda aka yi garkuwa da su bayan wani kwanton bauna a tun watan Yunin da ya gabata.