• English
  • Business News
Tuesday, July 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mayakan Ukraine Na Gudu Daga Fagen Fafafata Wa Da Rasha

by Rabi'u Ali Indabawa
3 years ago
in Labarai
0
Mayakan Ukraine Na Gudu Daga Fagen Fafafata Wa Da Rasha
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Wasu daga cikin sojojin Rasha na kin komawa fagen daga domin yin yaki a Ukraine saboda abubuwan da suka fuskanta a baya a fagen yaki a lokacin kutsen farko da Rasha ta yi wa Ukraine, kamar yadda wani lauya mai kare hakkin bil’adama na Rasha ya bayyana.

“Ba na so na koma Ukraine domin na kashe ko a kashe ni,” in ji Sergey – ba shi ba ne ainahin sunansa ba – wanda ya shafe makonni biyar yana yaki a Ukraine a farkon shekarar nan.

  • Wata Budurwa Ta Shirya Tsaf Don Auren Kanta A Indiya

Yanzu ya koma gida Rasha, bayan ya samu shawarwari daga lauyoyi domin ya guje wa mayar da shi fagen daga. Sergey na daya daga cikin daruruwan sojoji da aka gano cewa sun dauki irin wannan shawara.

Sergey ya ce ya shiga matsananciyar damuwa sakamakon abubuwan da ya fuskanta a Ukraine.

“Ni na dauka mu ne sojojin Rasha, wadanda suka yi fice a duniya,” in ji matashin a lokacin da yake bayani a cikin fushi. A maimakon haka, sai ake ganin za su iya yaki ba tare da wasu muhimman kayan aiki ba, kamar irin su gilashin gani da dare, in ji shi.

Labarai Masu Nasaba

Yanzu-Yanzu: Majalisa Ta Amince Wa Tinubu Ciwo Bashin Dala Biliyan 21

Natasha Ta Koma Majalisar Dattawa Duk Da Tsaurara Tsaro

“Mun koma kamar ‘ya’yan magen da ba su gani.
Mun tsorata da rundunarmu. Ba wasu kudi sosai za a kashe ba domin wadata mu da makamai. Me ya sa ba a yi haka ba?”
Sergey ya shiga aikin soja ne bayan an tursasa masa – akasarin matasa na kasar Rasha wadanda ke tsakanin shekaru 18-27 dole ne su yi aikin soja na tilas na shekara guda. Amma bayan watanni kalilan da ya soma, sai ya saka hannu kan kwantiragi da zai ba shi dama ya ci gaba da aikin har na tsawon shekara biyu inda kuma zai samu albashi.

A watan Janairu, an tura Sergey kusa da iyakar Rasha da Ukraine inda aka fada masa cewa wani atisaye ne za su yi. Bayan wata guda, a ranar 24 ga Fabrairu, ranar da Rasha ta kaddamar da yaki kan Ukraine aka fada masa cewa ya tsallaka iyakar kasarsa. Kusan nan take sai aka soma kai wa rundunarsa hari.

A daidai lokacin da suka yada zango da dare a wata gona da ba a nomawa, sai kwamandan su ya ce: “A yanzu irin aikin da kuka yi zuwa yanzu, wannan ba wasa bane.”
Sergey ya girigiza matuka
“Abin da na fara tunani shi ne ” Da gaske wannan na faruwa da ni?”
An ta kai musu hare-hare da bindiga,” in ji shi a lokacin da suke tafiya da kuma lokacin da suka yada zango. A cikin rundunarsu mai dauke da sojoji 50, an kashe mutum goma an kuma raunata 10. Kusan duka sojojin da ke tare da shi ba su wuce shekara 25 ba.

Ya ji labarin wasu daga cikin sojojin Rasha wadanda ba su san makamar aiki ba wadanda ba su san ma yadda za su harba bindiga ba kuma ba su san kan yadda roka take ba, ba su san gaba da bayanta ba”.
Ya ce ayarin motocin da suke ciki da ke tafiya tun daga Arewacin Ukraine ya rabu bayan kwana hudu a yayin da wata gada da za su tsallake bam ya tashi da ita, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar abokan yakinsu.

A wata mai kama da haka, Sergey ya bayyana cewa dole ne ya wuce wasu daga cikin abokansa da ke konewa a cikin wata mota da suka makale a cikinta.

“Gurneti ne ya tayar da motar. Sai ta kama da wuta kuma akwai sojojin Rasha a ciki. Mun ta tafiya a kusa da ita a lokacin da ake bude mana wuta. Ban kalli ko baya ba.”
Sai rundunarsa ta ci gaba da tafiya ta gefen iyakar kasar, amma a bayyane take akwai karancin dabara a tattare da su, in ji shi.

Sojojin da za su taimaka musu sun ki isowa kuma ba su da kayan aikin da za su tunkari aikin da ke gabansu na kwace babban birni.

“Sai muka ci gaba da aiki ba tare da jirgi mai saukar ungulu ba, muna tafiya a jere tamkar muna zuwa wurin fareti.”
“Sai muka yi sauri muka tafi ba tare da zama da dare ba kuma ba tare da mun je zagaye ba. Ba mu bar kowa a baya ba, idan wani ya yi kokarin bi ta bayanmu ya kai mana hari babu wanda zai kare mu.
“Ina tunanin kusan duka mutanenmu sun mutu. Da a ce mun tafi a hankali yadda ya kamata, kuma da mun duba kan hanya ko da an dasa nakiyoyi, da an kaurace wa mace-mace.”

Kokawar da Sergey ya yi kan batun karancin kayayyakin aiki ta fito ne a yayin wata tattaunawa ta waya wanda ake zargin an yi ta ne tsakanin sojan Rasha da iyalansa, wanda rundunar tsaron Rasha ta yi kutse a cikin kiran wayar kuma ta wallafa tattaunawar da suka yi.
A farkon watan Afrilu, an tura Sergey zuwa kan iyakar kasar kuma zuwa wani sansanin Rasha. An janye sojoji daga Arewacin Ukraine inda ake ganin suna hada kansu domin su kaddamar da hare-hare a gabashin kasar. Daga baya a cikin watan, sai aka ba shi wani umarni na ya koma Ukraine, inda ya shaida wa kwamandansa cewa bai shirya zuwa ba.

“Sai ya ce hakkina ne. Ba su yi ma kokarin su shawo kaina ba, saboda ba mu bane na farko,” kamar yadda Sergey ya bayyana.
Wani lauya ya shaida wa Sergey tare da wasu mutum biyu da su mayar da makamansu su kuma koma shedikwatarsu, inda za su rubuta takarda da za su yi bayani kan cewa sun gaji da wannan aiki kuma ba za su iya ci gaba da yaki a Ukraine ba.

An shaida wa Sergey cewa ya koma rundunarsa kuma hakan na da muhimmanci sakamakon idan ya tafi, hakan tamkar ya gudu ne daga filin daga wanda hakan zai iya ja a daure shi tsawon shekara biyu.

Kwamandojin sojoji na yawan kokarin bude ido ga sojoji masu aikin kwantiragi domin su tsaya a rundunoninsu, kamar yadda wani lauyan kare hakkin bil adama a Rasha Aledei Tabalob ya bayyana.
Sai dai ya bayyana cewa ka’idojin aikin soja a Rasha ba su amince da batun mutum ya ki yarda ko kuma ya ce ba zai je yaki ba idan ba ya so yaje.

Mai kare hakkin bil adama Sergei Kribenko ya bayyana cewa ba shi da masaniya kan wata doka da ke aiki kan wadanda suka ki yarda su koma fagen daga.

Hakan na nufin ba a taba kokarin kama wani da laifi ba.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Ya Kamata Buba Marwa Ya Yaki ‘Yan Siyasa Masu Raba Wa Matasa Kwaya – Matasan Arewa A Kudu

Next Post

Dauda Lawal: Abubuwa 12 Game Da Dan Takarar PDP A Zamfara

Related

Yanzu-Yanzu: Majalisa Ta Amince Wa Tinubu Ciwo Bashin Dala Biliyan 21
Manyan Labarai

Yanzu-Yanzu: Majalisa Ta Amince Wa Tinubu Ciwo Bashin Dala Biliyan 21

3 hours ago
Natasha Ta Koma Majalisar Dattawa Duk Da Tsaurara Tsaro
Manyan Labarai

Natasha Ta Koma Majalisar Dattawa Duk Da Tsaurara Tsaro

6 hours ago
Rayuwata Na Cikin Hatsari, A Dawo Min Da Jami’an Tsarona – Natasha 
Manyan Labarai

Rayuwata Na Cikin Hatsari, A Dawo Min Da Jami’an Tsarona – Natasha 

7 hours ago
Ban Tsani Buhari Ba, Ina Sukar Sa Ne Kawai Kan Matsalar Tsaro – Ortom
Manyan Labarai

Ban Tsani Buhari Ba, Ina Sukar Sa Ne Kawai Kan Matsalar Tsaro – Ortom

10 hours ago
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP
Manyan Labarai

Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

12 hours ago
Tsohon Sakataren Gwamnatin Bauchi, Ibrahim Kashim, Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Manyan Labarai

Tsohon Sakataren Gwamnatin Bauchi, Ibrahim Kashim, Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

13 hours ago
Next Post
Dauda Lawal: Abubuwa 12 Game Da Dan Takarar PDP A Zamfara

Dauda Lawal: Abubuwa 12 Game Da Dan Takarar PDP A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Tana Da Dokoki Da Ka’idoji Sama Da 180 Dake Kare Nakasassu

Kasar Sin Tana Da Dokoki Da Ka’idoji Sama Da 180 Dake Kare Nakasassu

July 22, 2025
Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Doke Afrika Ta Kudu

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Doke Afrika Ta Kudu

July 22, 2025
Karin Maganar Sinawa: Koyar Da Su Ya Fi Bayar Da Kifi

Karin Maganar Sinawa: Koyar Da Su Ya Fi Bayar Da Kifi

July 22, 2025
Sin Ta Samar Da Karin Guraben Aikin Yi Miliyan 6.95 A Rabin Farko Na Bana

Sin Ta Samar Da Karin Guraben Aikin Yi Miliyan 6.95 A Rabin Farko Na Bana

July 22, 2025
Yanzu-Yanzu: Majalisa Ta Amince Wa Tinubu Ciwo Bashin Dala Biliyan 21

Yanzu-Yanzu: Majalisa Ta Amince Wa Tinubu Ciwo Bashin Dala Biliyan 21

July 22, 2025
Sin Da Masar Za Su Karfafa Dangantakarsu Karkashin Kungiyar SCO

Sin Da Masar Za Su Karfafa Dangantakarsu Karkashin Kungiyar SCO

July 22, 2025
Majalisar Dattawa Za Ta Yi Zama Na Musamman Don Karrama Buhari 

Majalisar Dattawa Za Ta Yi Zama Na Musamman Don Karrama Buhari 

July 22, 2025
Natasha Ta Koma Majalisar Dattawa Duk Da Tsaurara Tsaro

Natasha Ta Koma Majalisar Dattawa Duk Da Tsaurara Tsaro

July 22, 2025
Rayuwata Na Cikin Hatsari, A Dawo Min Da Jami’an Tsarona – Natasha 

Rayuwata Na Cikin Hatsari, A Dawo Min Da Jami’an Tsarona – Natasha 

July 22, 2025
Oshoala Za Ta Yi Ritaya Daga Buga Wa Nijeriya Ƙwallo

Oshoala Za Ta Yi Ritaya Daga Buga Wa Nijeriya Ƙwallo

July 22, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.