Zahra Muhammad da aka fi sani da Zahra Bentures, matashiyar ‘yar kasuwa ce a fannin fasahar zamani da kware wajen aika kayan kasuwarta ta hanyoyin intanet daba-daban, ta yi wa wakiliyar LEADERSHIP Hausa Amina Bello Hamza bayanin yadda yadda ta tsinci kanta a harkar kasuwanci da kuma yadda take tafiyar da shi. Sannan ta ja hankalin mata musamman masu aure kan su tashi su nemi na kansu, kada su dogara da abin da maigida zai rika basu, domin a cewarta su kansu mazan yanzun ba sa sanin matan da suke zame musu jidali a rayuwarsu ba, ga dai yadda ganawar tasu ta kasance.
Da Farko za mu so ki bayyana mana sunanki
Sunana Fatima Abdurrashid Muhammad, amma wasu sun fi sani na da Zahra Muhammad ko Zahra Bentures musamman a Facebook. Ina zaune a Garin Samaru Zariya, Kaduna. Ni daliba ce kuma ‘yar kasuwa mai tasowa. Na yi karatu tun daga matakin firamare har zuwa jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Ko malamar na da aure?
A a ba ni da aure
Wace sana’a kike yi a halin yanzu?
Ina gudanar da sana’a ta a karkashin kamfaninmu mai suna ZB Global Bentures, inda nake sayar da garin Danwake, yaji, da sauran abubuwan amfanin gida. ZB Data wani sashi ne na ZB Global Bentures in da muke saida Data, Airtime, Electricity Bill, Bulk SMS, Edam pin da sauran su. Muna da website (www.zbdata.com.ng) tare da application (zb Data) wanda mutum zai iya saukewa a play store domin ya fara sanar sayar da data, kati da sauransu.
Mene ne ya baki sha’awar fara wannan sana’a?
Gaskiya na ji dadin wannan tambayar sosai, wato ba komai bane ya sa na ji ina sha’awar sana’a ba illa son na ga burina ya cika. Don gaskiya ba wai na taso gidanmu na ga ana sana’a bane, ba ni mantawa lokacin da zan shiga jami’a takardu na bangaren kiwon lafiya na cika, a tunani na zan samu damar taimaka wa mutane a asibiti zan hadu da mutane daban-daban to sai dai Allah bai sa na samu ba, a nan ne na fara tunanin mafita, ta ya zan cimma burina, kawai sai na fara tunanin sana’a domin zan samu damar haduwa da mutane daban-daban, kuma zan tara kudin da zan iya taimaka wa al’umma. Amma akan hanyar na fahimci sana’a ta wuce yanda nake kallon ta na koyi abubuwa da daman gaske, na fahimci ba wai iya dan a tara kudi ko a hadu da mutane ba ake sana’a na kara samun dalilan da zai sa na ci gaba da sana’a ta domin ina jin dadin abin da nake tana kawo min kwanciyar hankali, debe kewa da jin dadi.
Idan mutum na son fara wannan sana’ar wane abu zai tanada don samun cikakkiyar nasara?
Eh to da farko dai kusan kowace sana’a ana bukatar jari, kamar kasuwancin data ko da Naira 2,000.00 mutum zai iya farawa, website da na fada a baya shi mutum zai zauna ya bude asusun, ko aje play store a sauke bayan shi kuma, mutum zai sa kudi a wallet shike nan sai ya fara sayarwa kwastomomi ana biyan sa, yana cin riba.
Wace shawara kike da shi ga al’umma?
Shawara ta ita ce duka maza da mata su tashi su nemi abin yi, yanayin ya canja musamman mata kar su zauna su nade hannu su ce komai sai an yi musu, don gaskiya idan ba su kai zuciya nesa ba sun ta ganin bacin rai, to abin duniyar ne ba isa yake ba, kuma su kan su mazan yanzun ba su san matan da za su zame masu jidali, akalla dai mace ta san dubarun nema na abin da ba’a rasa ba ya zama za ta iya daukewa kanta ba don ba za a iya yi mata ba, kuma akalla tana da dangi da za ta yi wa alheri ‘yan uwa da abokan arziki kin ga sai ta nema ne duk za ta iya wannan aikin ladan. Ya kamata a wurin nema mu dinga kallo da yin koyi da nana Khadija matar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama. Kuma ya zo cikin hadith cewa wajibi ne ga dukkan Musulmi ya nemi halal.
Menene burinki a wannan sana’ar taki?
Babban burina a sana’a ta shi ne na ga ya fadada ta hanyar samar wa Kowane nau’in mutum abin da ya fi dacewa da lafiyarsa wanda ya fi bukata, na samu na yi masa rijista da NAFDAC da sauran hukumomin da ya dace su sa hannu a kai, kuma na mallaki wurin da zan rika aje kayan hatsi kafin da bayan an sarrafa, na mallaki abin da zai saukaka min wurin zirga-zirga. Kuma nan gaba kadan ya zama har fitarwa waje za’a iya yi na kayanmu, na samu abubuwa mafi kyau da inganci.