Jami’in ba da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Tom Fletcher, ya fitar da Dalar Amurka miliyan 5 daga Asusun Ba da Agajin Gaggawa (CERF) don daukar matakan da suka dace na magance ambaliyar ruwa a Nijeriya.
Jami’in kula da ayyukan jin kai na MDD a yankin, Mohammed Malick Fall, ne ya bayyana hakan a ranar 12 ga Fabrairun 2025, a Abuja.
- Dole Ne A Bai Wa Al’umma Damar Mallakar Kananan Makamai Domin Kare Kansu – Shugaban DSS
- Kalaman Trump Marasa Kan-gado Game Da Gaza Za Su Kara Tsananta Halin Da Ake Ciki A Gabas Ta tsakiya
Samar da Dala miliyan 5 na CERF, ya dace da ƙoƙarin da Gwamnati ke jagoranta ta hanyar aiwatar da aikin da ake tsumayi.
Tawagar ta tattaro hukumomi da suka hada da hukumar kula da yanayi (NiMET), hukumar kula da ayyukan ruwa, da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa karkashin kulawar ofishin mataimakin shugaban kasa. Wannan yana tare da hadin gwiwar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai (OCHA).
A duk duniya, OCHA, wacce ke kula da CERF da Asusun Kula da Ruwa na Kasa (CBPFs) irin su Asusun Ba da Agajin Gaggawa (NHF), tana jagorantar matakai don taimaka wa miliyoyin mutane ta hanyar magance annoba kamar ambaliyar ruwa, fari, da kwalara.
A watan Oktoban 2024, CERF ta saki Dala miliyan 5 domin a kara kaimi wajen magance ambaliyar ruwa da kuma magance muhimman bukatu a jihohin Borno da Bauchi a yankin arewa maso gabas da Jihar Sokoto a arewa maso yamma. Kudaden CERF din ya cika dalar Amurka miliyan 6 da hukumar ta NHF ta ware (wanda ya hada da dala miliyan 2 domin daukar matakan da suka dace a dauka tare da yawaitar ambaliyar ruwa da ta raba kimanin mutum 400,000 da muhallansu a Jihar Borno. Ambaliyar ruwa ta lalata abubuwan more rayuwa tare da lalata daruruwan kadada na gonakin noma kafin girbi).
A cewar hasashen yanayi na 2025 da NiMET ta gudanar, ana sa ran fara damina a jihohin Arewa irin su Bauchi, Borno, Jigawa, Kano, Katsina, Sokoto, Yobe da Zamfara, tsakanin farkon watan Yuni da Yulin 2025. Wannan lokacin ya zo daidai da lokacin rani (a tsakanin girbi), lokacin da akafi samun karancin abinci sannan kuma farashin abinci mai gina jiki ke kara tashi. Shirye-shirye a kan lokaci game da wadannan abubuwa na da mahimmanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp