Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a Nijeriya ta jaddada kudirinta na yin aiki tare da kungiyar rajin ilimin ‘ya’ya mata, mai suna Malala Fund a kokarinta na magance kalubalen da ke hana miliyoyin yara, musamman ‘yan mata rashin zuwa makaranta.
A yayin wani taro da aka gudanar a Abuja tare da bada lambar yabo ta Nobel Laureate da Malala Fund, Ms. Malala Yousafzai, tare da tawagar kungiyar, mai kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya, Mr. Mohamed Malick Fall, ya jaddada sadaukarwar Majalisar Dinkin Duniya na bunkasa ilimi mai hade da daidaito ga kowa.
- Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
- Fim Na Nezha 2 Na Kasar Sin Ya Kara Samun Lambar Yabo
“Majalisar Dinkin Duniya ta sake jaddada goyon bayanta ga Malala Fund wajen ciyar da ‘ya’ya mata da samun ingantaccen ilimi, ba za a bar wani yaro a baya ba,” in ji Fall.
Mista Fall ya jagoranci tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ta kunshi wakilai daga UNICEF, UNESCO, UNDP, UNFPA, da mata na Majalisar Dinkin Duniya a wajen taron. Ya jaddada cewa canjin al’umma ya ta’allaka ne akan jarin dan’Adam musamman ta hanyar ilmantar da ‘ya’ya mata da karfafa wa mata.
Ya kara da cewa, “tare da gwamnati da abokan huldarmu, mun himmatu wajen kawar da duk wani cikas da ke hana yara, musamman ma masu rauni damar samun ilimi”.
Fall ya gano muhimman abubuwan da ke kawo cikas ga ilimi a Nijeriya, da suka hada da rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki, sauyin yanayi, da kuma ka’idojin zamantakewa da al’adu. Ya yi kira da a kara himma wajen inganta daidaiton jinsi da karfafa hadin kan al’umma a matsayin muhimman hanyoyin samun ci gaba mai dorewa.
Malala, wacce ta isa Abuja a ranar 26 ga watan Satumba don taron shekara na Hukumar Kula da Malala Fund, ta nanata rawar da Nijeriya ke takawa a dabarun duniya na Malala Fund na 2025 zuwa 2030.
“Nijeriya kasa ce mai fifiko ga Malala Fund, tun daga shekarar 2014, mun zuba jarin sama da dala miliyan 8 ga kungiyoyin hadin gwiwa na Nijeriya da ke kokarin dakile hana yara mata zuwa makaranta,” in ji ta.
Ta zayyana dabaru na Malala Fund a Nijeriya, wadanda suka hada da: tabbatar da cewa ‘yan mata masu aure da masu juna biyu za su iya komawa makaranta; habaka tallafin ilimi da tabbatar da biyan bukatun ‘yan mata; da kuma amfani da ilimi a matsayin hanyar warware matsalar auren yara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp