Jiya Jumma’a 10 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar Sin, Wu Qian, ya kira taron manema labarai a wajen shawarwarin Shangri-La ko kuma SLD a takaice a kasar Singapore, inda ya bayyana yadda aka gudanar da shawarwarin ministocin tsaron kasashen Sin da Amurka.
Wu ya ce, a yayin shawarwarin, ministan tsaron kasar Sin, Wei Fenghe, ya jaddada matsayin kasar Sin kan batun Taiwan, inda ya ce, Sin kasa ce daya tilo a duniya, kuma Taiwan wani yanki ne da ba za’a iya balle shi daga kasar Sin ba. Manufar kasancewar kasar Sin daya tilo a duniya, tushen siyasa ne na alakokin Sin da Amurka, kana, amfani da batun Taiwan don kawo cikas ga ci gaban kasar Sin ba zai kai ga nasara ba.
Minista Wei ya ce, kwanan baya, kasar Amurka ta sake sanar da cewa za ta sayar da makamai ga yankin Taiwan, al’amarin da ya sabawa manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, gami da ka’idojin sanarwar hadin-gwiwa uku na kasashen biyu, da lalata cikakken yankin kasar Sin da moriyar tsaronta, kana lamarin ya lalata dangantakar Sin da Amurka da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan. Kasar Sin ta nuna adawa gami da yin Allah wadai da irin wannan batu.
Wu Qian ya ce, minista Wei ya jaddada cewa, in dai akwai wanda ke yunkurin balle Taiwan daga kasar Sin, babu tantama rundunar sojan kasar Sin za ta mayar da martani don tona asirinsu, da kiyaye cikakken yankin na kasar Sin.
Wu Qian ya kara da cewa, dangane da batun tekun kudancin kasar Sin, minista Wei ya ce, kasashen dake wannan yankin, suna da niyya da hikima gami da kwarewa sosai wajen daidaita batutuwan da suka shafi tekun kudancin kasar Sin. Shisshigin da kasashen da ba na wannan yanki ba suka yi, shi ne ke kawo rashin tabbas. Ya dace kasar Amurka ta dauki matakai a zahiri don amfanawa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudancin kasar Sin, maimakon rura wutar rikici da tunzurin neman haifar da fito-na-fito.
An kaddamar da shawarwarin Shangri-La (SLD) karo na 19 a kasar Singapore a jiya Jumma’a, inda memban majalisar gudanarwa na kasar Sin, wanda kuma shi ne ministan tsaron kasar, Wei Fenghe ya halarci shawarwarin, da halartar tattaunawa da takwaransa na Amurka, Lloyd Austin. (Murtala Zhang)