A cikin shekarar 2024 da ta gabata, Amurka ta sha samarwa Isra’ila da Ukraine tallafin makamai, ta zama mai haifar da tashin hankali a duniya.
Amurka ta dorawa sauran kasashe matsalar bashinta ta hanyar sayar da kudin yanar gizo na Bitcoin, inda ta zama mai dana tarkon bashi ga sauran sassa.
Ban da wannan kuma, Amurka ta sha tsoma baki cikin harkokin gida na sauran kasashe. Alal misali, ta nuna fuska biyu game da batun yankin Taiwan wanda ya kasance harkar cikin gidan kasar Sin, kana tana ta rura wutar rikici a wasu yankuna.
Don kiyaye moriyar kanta, Amurka ta kan yi amfani da haraji a matsayin makami mai karfi, don dakile sauran kasashe ciki har da kawayenta.
Amurka tana ikirarin kiyaye hakkin Bil Adam da demokuradiya a duniya, amma abin da take yi ya sabawa hakan, inda sha tada zaune tsaye a wasu yankuna, ba tare da yin la’akari da yanayin da jama’ar yankunan ke ciki ta fannin hakkin bil Adam da demokuradiyya. Ko ina alkawarin nata?