A ranar Lahadi ne mahukuntan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars suka bayar da sanarwar dakatar da mai koyarwa, Usman Abdallah mako uku, sakamakon rashin kokarin kungiyar a baya bayan nan a bana da kuma nuna halin rashin hakuri ga magoya bayan kungiyar a lokacin da aka tashi daga wasan da kungiyar ta tashi canjaras da kungiyar Bayelsa United a filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata a Kano.
A wata sanarwa da aka fitar a shafin sada zumunta na facebook, kungiyar ta ce kociyan ya nuna halin rashin da’a, bayan tashi ba ci a wasa da Bayelsa ba kuma halayyar da ya nunawa magoya baya ba ta dace ba saboda a matsayinsa na mai koyarwa dole ne sai ya jure duk wani surutu da magoya baya za su yi masa. Pillars ta kasa hawa kan ganiya a ‘yan wasannin baya bayan nan, wadda ta yi nasara daya daga karawa uku a gasar ta Premier Nijeriya.
- Ayyukan Jami’an Ilimi Da Muhimmancinsu (6)
- Saudiyya Ta Yi Watsi Da Shirin Fitar Da Falasdinawa Daga Gaza
Hakan ne ya sa shakku ga mahukuntan Pillars da magoya baya kan rashin kokarin kungiyar da abin da hakan zai haifar kuma bayan tashi daga wasan da Bayelsa a wasan mako na 24 ranar Lahadi, mahukuntan suka ce ba za su lamunci rashin da’a daga Usman Abdalla ba da ya yi wa magoya bayanta, hakan ya sa aka dauki mataki a kansa kuma ya fara aiki nan take.
Tuni aka bai wa Ahmed Yaro-Yaro aikin rikon kwarya, inda Abubakar Musa da Gambo Muhammad da Suleiman Shu’aibu da kuma Ayuba Musa za su taimaka masa. Kano Pillars za ta je Remo Stars a wasan gaba na mako na 24 a babbar gasar firimiya ta Nijeriya.