Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin TASKIRA, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewa aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi tsiyacewar ma’aikata bayan kammala aiki. Da yawan wasu mutanen wadanda suke da ofis, ko mukamai, ko siyasa, ko aikin gwamnati, bayan wasu lokuta kalilan sai su tsiya ce. Shin a ina matsalar take, me yake janyo hakan?, wadanne hanyoyi ya kamata abi domin magance afkuwar hakan?”.
Shafin TASKIRA ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu.
Ga dai bayanan nasu kamar haka;
Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To maganar gaskiya abubuwan dake jawo hakan suna da yawa amma wasu daga ciki akwai azurta kai da dukiyar al’umma ko kuma na ce haram, domin ita haram kadan tana latata dukiyar halak komai yawan ta, sai kuma na biyu akwai (Ludury life) ma’ana gina rayuwar yau da kullum akan karya ko kuma bukatar da tafi karfin samun mutum a lokacin daya bar aiki ko kuma ya sauka daga mukamin da’aka zabe shi ko nada shi. To da farko dai ya kamata mutum ya tasftacce hanyar neman abinci ko kuma nace hanyar tara dukiyar, domin hakan zai taimaka wajen dukiyar tayi albarka, sai kuma na biyu ya kamata mutum yayi rayuwa daidai gwargwado kada mutum yake hidimar data wuce samunsa ko kuma almubazzaranci lokacin da yake aikin ko kuma rike da mukamin siyasa. To ya kamata mutum yake kokari wajen tasftacce nemansa a duk lokacin da mutum ya samu wata dama ta aikin gwamnati ne ko mukamin siyasa domin babu wani da yake dorewa a rayuwa don haka ya kamata mutum yayi taka-tsan-tsan.
Sunana Fateema Musa Muhammad Kawu Lambu, Jihar Kano:
Akwai mutane da yawa dake rike da mukamai a ofisoshi, siyasa, ko aikin gwamnati da bayan wani lokaci sai su tsiyace su rasa komai. Abin da yake kawo hakan rashin kyakkyawan tanadi na kudi da zuba jari, dogaro da matsayin aiki kawai ba tare da neman hanyoyin kudin shiga masu dorewa ba, rashin koyi da dabi’un kyautata rayuwa da adana kudi, cin hanci da rashawa da ka iya kaiwa ga bincike da rasa matsayi, mugun tarayya ko shawarwari marasa kyau daga abokai ko dangi. Hanyoyin magance matsalar; Samar da dabarun tanadi tun kafin mutum ya bar mukaminsa, koyi da sana’o’i ko zuba jari da zai taimaka bayan barin aiki, rayuwa cikin tsari da nisantar almubazzaranci, tsayawa kan gaskiya da kaucewa cin hanci ko rashawa. Shawara ga masu mukamai da ma’aikata; Ayi tunani da shiri tun kafin lokaci ya kure, ayi amfani da albashi da alawus wurin zuba jari mai kyau, a guji yin rayuwa fiye da yadda ake iya jurewa, a tsaya kan gaskiya don gujewa matsalolin shari’a a nan gaba.
Sunana Alhassan Abdulrahman Bununu Tafawa Balewa A Jihar Bauchi:
A gaskiya abun da ke janyo faruwar hakan shi ne rashin tsaida gaskiya yayin da mutum yake gudanar da aikinsa na siyasa, kasuwanci, ofis dama sauransu. Idan wani ya sami damar da zai taimaka ma wani kana samar da aiki sai ka ga wai sai an bashi rashawa in ba’a bada ba sai ka ga wannan slot din ya wuce bayan yana da ikon bada shi, to ka ga wannan kudin da yake tarawa ta wannan aiki ko harkar a wannan lokaci zai ga Kamar ba za ta kare ba, amma sakamakon rashin albarkar dukiyar sai ka ga ta kare wanda ka karbi kudin a gunsa kuma ka ga ya fika walwala da kwanciyar hankali. Ga ‘yan siyasa kuma hakkokin mutanen da suke shugabanta da kuma kudaden yankunansu da ake basu suke ci suma suna sauka bada jimawa ba za su fara girban abun da suka shuka. Allah ya sa mu dace. A gaskiya hanyar da za a magance hakan shi ne kawai mu gyara halayenmu da kuma jin tsoron Allah mu tuna wannan kudaden duk dadinsu na wani lokaci ne. Ita kuma gwamnati take tallafawa ma’aikatanta wajan biyansu albashi mai inganci wanda zai shi mutum da iyalansa sabida a kan sami sauyin yanayi wantashin kayayyaki. Kokuma takebasu salarinsu akan lokuta dan suma su samu nutsuwa. Shawarata a nan shi ne kowani mai mukamin gwamnati ko siyasa ko ‘yan kasuwarmu muke jin tsoron Allah a cikin lamuranmu mu sani idan muka sawwaka musu muma Allah sai ya sawwaka mana Allah ya sa mu dace Ameen.
Sunana Fatima Ya’u Ado daga Jihar Kano:
Abin da yake janyo tsiyacewarsu shi ne rashin gaskiya da rikon amana da cin hanci da rashawa. Yadda za a magance shi ne su daina cin hanci da rashawa, su kasance masu gaskiya da rikon amana a ko’ina.
Sunana Comrade Muhammad Isah Zareku Miga A Jihar Jigawa:
Abun da yake sa wasu mutane da zarar sun rasa mukami ko mulki na siyasa ko wani ofis sun tsiya ce magata gaskiya Rashin adalcin sune, kuma shi dama Hausawa na cewa Alhaki kwi-kuyo ne. Hanyar magance wannan matsalar ita ce masu Mulki ko ofis ko mukami na Siyasa su yi adalci a mukaminsu, su san cewa ranar gobe kiyama Allah zai tambaye su. Shawarata a nan shi ne duk lokacin da za a bawa wani mukami a tabbatar a harsashe zai iya kwatanta adalci a harkokin mukaminsa, sannan kuma a samu wanda yake da ilimin addini dana zamani.
Sunana Khadija Musa Muhammad Jihar Kano:
Ni dai a iya fahimta ta daman aikin wata-wata ba aikin yi bane, dan ban taba lissafa shi a matsayin sana’ar yi ba ko nawa mutum yake samu, hasalima ga masu bincike koffofi da basira sun tabbatar da cewa duk wanda yayi kudi da aikin wata kusan bada guminsa ya tara wannan kudin ba, shi ya sa in sun sauka da mukami shi daman can sun saba da kashe-kashe da yawan kasashi duk da suna kokari wajan siyan kadara to da sun sauka sai su koma kan kadara suna siyarwa sabida biyan bukatunsu. Shawarar da zan bayar ita ce; su rika fara yin kasuwanci a lokacin da suke aikin, a lokacin da suna aiki yadda koda sun bar aikin baza su sha wahala ba.
Sunana Halimat sani Muhammad (DIetician Arfah), Rijiyar Lemo Jihar Kano:
Dogaro da matsayin aikin kawai ba tare da neman wasu hanyoyin samun kudinba. Cin hanci da rashawa yana iya sa ka zama koma baya lokaci daya, Almabarzaranci da rashin tanadi. Hanyoyin daya kamata a magance matsalar; Fara sana’o’in dogaro da kai, ko zuba hannun jari wanda zai taimakawa mutum koda ya bar aikinsa, Yin rayuwa cikin tsari da daina Almabarzaranci, Rike gaskiya da amana, gujewa cin hanci da rashawa. Shawara ga ma’aikatan gwamnati da masu mukamai, da ‘yan siyasa;. Ayi amfani da albashi mai tsafta ka rasa kudin haramun wurin yin kasuwanci ko zuba hannun jari, a tsaya kan gaskiya da amana a harkar kasuwanci, a yi rayuwa daidai karfi kar’ace za a yi rayuwar da tafi karfin mutum.
Sunana Lawan 𝗜sma’il (Lisary Rano) Rano LGA Jihar Kano:
Wasu kaddararsu ce a haka, wasu kuma sharrin da suka yi ne a lokacinsu ya biyo su. Hanya ta farko duk wanda ya sami dama daya ko kuma dukan irin wannan abubuwa da aka lissafo a sama to maganar gaskiya ka tsaya kayi abin da ya dace kada ka ga ka sami dama kayi abin da ba na daidai ba, domin duk abin da kayi to ka sani tun a nan duniya za ka fara girba. Shawarata a nan ita ce mu ji tsoron Allah mu daina amfani da wata dama domin gallazawa wasunmu domin duniya ba madawwama ba ce, mu ji tsoron Allah akan dukkan wani hali da muka tsinci kanmu. Allah ya sa mu dace.
Sunana Muhd Uba Jihar Kano:
Ya kamata su maida hankali gurin neman halak domin Allah shi yake da arziki ko tsoyacewa, Allah ya sa mu dace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp