Kamar kowane mako shafin TASKIRA na zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu. Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi ma’aurata musamman fannin kwalliya wanda wasu matan suke kasa yinta yayin da suka kwan biyu a gidan miji ko aka saba da mijin. Dalilin hakan shafin TASKIRA ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; ‘Ko me yake kawo hakan?, wadanne irin matsaloli hakan ka iya haifarwa?’
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar Kano Rano LGA:
Shirme da shashanci da rashin sanin kai irin na matanmu hausawa mana. Suna da yawa domin sukan kawo saka namiji karin aure wasu mazajen ma wadanda basa tsoron Allah hakan yake sa su fadawa zinace-zinace. Shawarata a nan ita ce gaskiya wadanda suke irin wannan su daina su dawo yin kwalliya fiye ma da tana budurwa, domin ta sani tsuntsu biyu take jifa a hakan ga lada da za ta samu ga kuma janyo hankalin mijin nata zuwa gareta gudun kada ya fada ga matan banza a waje. Wadanda suke yin kwalliya a gidajen mazansu kuwa su ci gaba domin hakan ma ya kan kara dankon so da kauna a wajen mazansu. Allah ya sa mu dace amin
Sunana Fatimah Zahra Mazadu Daga Jihar Gomben Nigeria:
Ba abun da ke janyo haka sai sakaci da rashin wayo, ta wani fannin kuma aljihu da halin maza dan suma suna nan a gari, za ka ga wata ta birgeka amma taka ta gida ka gagara kashe mata dan tayi kyau, sannan ba yadda za a yi kina kara girma kina komawa jeji, ai a lokacin da ki ka dade da namiji a lokacin ne ya kamata ki kara wanka akan wanda ki ke dan maida hankalinsa kacokam a kanki, tsabta naki kwalliya naki jan hankali naki. Na daya zai fara hangen na waje, na biyu zai dinga nisanta dake, ko da ko ba mai ra’ayin kwalliya sosai bane, ba zai so ace kin daina kwata-kwata ba, ajinki zai ragu a gareshi, hangen sabon aure zai daka tsalle ya shige zuciyar shi da sauransu. Kar mace ta kuskura tayi aure ya janye daga mijinta ta fannin kwalliya saboda shi ne ake kira da jagoran da namiji shi ke janye hankalin namiji sosai, dan ba namijin da baya son kwalliya ke kanki in kina kwalliya kin fi jin dadin kanki ko a cikin mata ‘yan uwanki bare a gaban miji, mace mai kwalliya ita ce ta nunawa a idon duniya, ta gaban mota, cikekkiyar mai iko da kasaita, gangariya tauraruwa a cikin mata, duk wacce take da wannan niyyar wai dan kin auri namiji me ya saura? to, wallahi akwai gwarama ki gyara dan gwagwarmayar gidan auren ya fi na waje, ai nanne ma za ki zage ki kara burge shi ya ji ya matsu kullum ya zo ya ga kwalliyar ki, mai sanyaya masa zuciya mai dauke da linkin sonki da kaunarki, mata a daure a dinga kwalliya.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya rashin ilimin zaman aure ne ke jawo haka, domin yin tsafta ko kwalliya ga matar aure yana matukar kara kauna da soyayya a tsakaninta da mijin ta, kuma zai taimaka wajen ta mallake shi gabadaya ya daina hangen wata mace sai ita kadai. To farko dai hakan yana jawo ake samun sabani tsakanin macen da mijin ta a lokuta da dama wanda hakan ka’iya kawo tabarbarewar dangantaka a zamansu na aure, kuma hakan yana iya zama silar mijin nata ya karo mata abokiyar zama ko kishiya koda kuwa ba shi da niyyar kara aure domin haka ne kadai zai zama mafita a gare shi. To shawara a nan ita ce ya kamata dai mata su sani tsafta daya ce daga cikin dabaru na mallake miji ba wai sai an hada da guru ko laya ba, kuma tsafta tana kara dankon soyayya da kauna a tsakanin ma’aurata, kuma uwa uba tsafta wani yanki ne na Imani wanda take taimakawa wajen samun cikakken addini.
Sunana Aisha T. Bello Jihar Kaduna:
Gaskiya ina jin haushin irin wanan matan gaskiya, na taba yi wa wata magana kan haka sai ta ce mani ai ni kwalliya ta yara ce wai ta barwa yara kuma ita da kanta ta fada mun mijinta na son kwalliya. Matsalar shi ne kawai zai kara aure kuma gun karan auren sai ki ga mai kwalliya. Shawara ta a nan ga masu irin wanan hali shi ne; kwalliya ba a tsufa da kwalliya yana bada girma sosai za ki ga ana kai ki inda baki kai ba kuma yana bada Personality.
Sunana Sadi Dauda Baturiya Jihar Jigawa:
Hakika wannan al’ada tana faruwa da ma’auratan wannan zamani na mu, kuma yin hakan yana da alaka da kiwa wato (ganda). Babu shakka yawaitar mutuwar aure a wannan zamanin yana da kazanta da sauran matsaloli makamantansu. Gaskiyar magana shawara ta ga matan wannan zamanin musamman sabbin aure su cire irin wannan tunanin na kazanta bayan tsafta domin kuwa rashin yin tsafta yana daga cikin abin da yake rage karfin soyayya tsakanin ma’aura
Allah ya kawo mana karshen matsalolin mutuwar aure a cikin al’ummar mu amin.
Sunana Fatima Nura Kila Jihar Jigawa:
Wasu laifin mazan ne wasu kuma na matan, wasu mazan daga an yi aure an dau wasu watanni ba zai iya siyan kayan kwalliyar da za ta yi ya ganta tsaf ba, wani kuma ko kudin sabulu bai badawa a nan kuma hankalin mace zai karkata a nan ta ga ita ba ta kwalliyar take ba, domin kudin abun kwalliyar da za ta siya ma babu. Yana haifar da matsaloli masu tarin yawa, a wannnan lokacin wani a nan yake ganin wata matar a waje ta birge shi tunda matar sa ba ta yin kwalliyar, sannnan ya kan rage shakuwa a tsakanin ma’aurata. Ya kamata mu mata mu dage koda mazajen mu basu yi mana ba mu, mu yi da kudin mu domin hakan ba karamar kima yake karawa ba a idon miji, domin kwalliya wata aba ce da ta ke karawa mata kyau, wadanda suke yi kuma su daina su rika yin kwalliya hakan zai kara masu shakuwa a tsakaninsu.
Sunana Anas Bin Malik Achilafia Yankwashi A Jihar Jigawa:
Wato idan muka kalli yadda ake rayuwa kafin aure da kuma bayan aure za mu fahimci cewa su matan suna mayar da kansu haka ne a dalilin ganin cewa an riga da an zama abu daya, ko da kwalliya ko babu hakan ba zai sa mijin ya kosa ba, tun da su mazajen ne kusan basa yabawa matan idan suka yi kwalliya, ko ado, sabanin kafin aure kusan kullum a cikin samun yabon namiji ta ke. Batun matsaloli kuwa akwai su; ta bangaren mace hakan yana mayar da ita koma-baya ta fuskar matsayinta a wurin miji, da kuma jawo mata kaskanci, da rashin wadata ta da kayan kwalliya, tunda miji ya ga ta daina yi. Ta bangaren miji kuma rashin yin kwalliyan yana sakawa ya ringa hange, ko gane-ganen wasu matan a waje, da suke cancara kwalliya abinsu. Ko da ba shi da niyyar kara aure hakan zai iya jan hankalinsa. Ina jan hankalin mata tare da basu shawara da su cigaba da yin ado da kwalliya ga mazajensu, ba sai idan za a fita ba, misali: kai tsaye kin san lokacin da mijinki yake dawowa gida ko da kuwa dare ne, ki saka kayanki masu kyau, ki chaba kwalliya, ki fesa turarenki mai kamshi, mijin na shigowa gida ya ganki a haka wallahi sai ya ji dadi a ransa, kuma za a cimma abubuwa da yawa daga hakan. Ina fatan a samu wata bayan karanta wannan bayani nawa ta gwada wannan siddabarun za ta sha mamaki.
Sunana Naja’atu Baffa Jihar Kaduna:
Wataran abin da yake janyo hakan ba komai bane face yawan aikace-aikace na gida na iya hana mace yin kwalliya da sauransu, kuma jigon wannan aikace-aikacen yara ne, saboda an mikawa ita wannan matar dafa musu abincin da za su ci, idan kananun yara ne yi musu wanka da shirya su, gyara ko’ina na gidan da dai sauransu, idan ta yi wankan ba lallai ta tsaya yin ado ba. Wataran kuma al’ada ce ke canja ra’ayin mace ko bada son ranta ba kamar hana mace kwalliyya da shiga mai kyau yayin da ta kai wadansu ‘yan shekaru. Matsalolin da hakan ya ke haifarwa su ne; hakan zai bi daga ‘ya’yayensu har zuwa ga jikokinsu a matsayin abin da ya dace, rashin girmamawa da kaskanci a wajen mazajensu da ma wadanda su ke mu’amala tare da su. Shawarar da zan bawa mata masu irin wannan tunanin ita ce; su zauna da mijinsu su tattauna wajen shawo kan matsalar idan aiki ne yayi mata yawa da sauransu, sannan akwai shirye-shiryen da ake yi na yanar gizo-gizo da dama na wayar da kan mata su ma su rinka sauraren shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp