Shafin Taskira shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacimmu na yau zai yi duba ne game da matan da suke gallaza wa yaran da aka bar musu amana ko kuma suke rike da su
Bara’atu Sani
Mata masu rike da yara da aka bar musu amana suna da muhimmiyar rawa a al’umma. Duk da haka, akwai wasu daga cikinsu da suke gallaza wa yaran ta hanyar nuna halin ko-in-kula, da cin zarafi, duka, ko kuma rashin samar musu da kulawa ta yau da kullum. Wannan matsalar tana bukatar a dauki mataki na gaggawa don kare rayuwar yaran da kuma tabbatar da cewa ana ba su tarbiyya mai kyau.
Muhimman Abubuwa:
- Hakkin Kulawa: Idan aka ba mace amanar yara, ya zama dole ta yi kokari wajen kyautata musu, tana bi da su kamar nata.
- Illar Gallazawa: Gallazawa yara na iya shafar lafiyarsu ta jiki da ta hankali, kuma tana iya haifar da matsaloli masu tsanani a rayuwarsu ta gaba.
- Hukunci: Doka ta tanadi hukunci ga wadanda ke cin zarafin yara. Ana bukatar iyaye da al’umma su sanya ido don tabbatar da cewa yara suna samun kulawa da kariya.
- Shawarwari: Idan mace ba ta da karfin iya daukar nauyin kulawa da yara, ya dace ta nemi taimako daga wajen iyaye ko kuma cibiyoyin tallafi na al’umma.
Taron dangi ne ya kamata domin magance wannan matsalar, ta yadda yaran za su girma cikin tsaro da jin dadi.
Suwaiba Aminu
To na farko de shi ne abin da yake janyo mata ke gallazawa yara wato wadanda aka bar mata su riko a iya kiran dan riko kamar dan miji ko wani da aka ce ka rike, to shi ne dai dan mijin da suka fi shan wahala a wajen mata.
Na farko dai wasu matan su kan fiskanci bambanci a wurin miji, shi namiji idan aka ce yau matarsa ta bar gida musamman in yaran da aka bari kanana ne koda da baya son su ba ya jan su a jiki ba ya kaunarsu, to da zarar mahaifiyarsu ba ta nan sai tausayinsu da kaunarsu sun yi tasiri a zuciyarsa, sai ya rika tausaya musu ya rinka fifitasu a kan ‘ya’yan da suke cikin gidan wadanda uwarsu take gidan, koda matansa sun kai uku a gidan sai ya rinka fifita wadannan yaran da babu uwarsu a gidan ya dinga tausaya musu. Kuma ba wani abu bane yake sa shi namiji ya rinka tausaya musu, tausayi ne na babu uwarsu a gidan shi ke sa su wadannan tausayin, kuma sannan ya dauki duk wata kolawarsa da damuwarsa ya dora akan wadanannan ‘ya’yan da babu uwarsu a gida. Sannan koda wani abu ne ya taso za ki ga kafin ya yi wa wadanda suke da uwa a gidan sai ya yi wa wadannan wadanda ba su da uwa a gidan saboda tausayi na ganin cewa su wadannan suna da uwa a gidan.
To su kuma mata da yawa abin da yake taka muhimmiyar rawa a zuciyarsu wurin tsana da tsangwamar ‘ya’yan rikon wannan shi ne mataki na farko musamman a wurin mata, tun da matan sun kasu kashi biyu zuwa uku, wasu mugwaye ne wasu kuma mutanan kirki ne.
Wannan dai idan an ci sa’ar macen da take rike ‘ya’yan mutuniyar kirki ce to miji shika lalatata, wannan mataki na farko yana fara jawowa ‘ya’yan tsana da tsaggwama.
Wasu kuma dama can mugwaye ne azzalumai, akwai kishi na uwa wanda wadansu sun zauna da uwar ‘ya’yan suna kishinta basa kaunarta, kishinnan da zafin kishi, idan aka ce babu uwar ‘ya’ya sai wannan kishin da zafin na uwa dajin zafi na uwa sai kuma a tattare a mai da shi kan ‘ya’ya, sai a zo ana azabtar da ‘ya’ya ta kowanne fanni ta kowanne bangare, wasu ma har su yi wa uban asiri ya kasance duk abin da za su yi wa ‘ya’yan uban ma ba zai taba gani ba.
To wasu kuma haka kawai ba ma su zauna da uwar ‘ya’yan ba amma haka kawai su zo su dauki karan tsana da tsaggwama su dora musu. Matan fa na gaya miki sun kasu kashi biyu wannan kashi na biyu ne na gaya miki.
Kaso kuma na uku su kuma su ne wadanda suka dauki gaba daya ma ‘ya’yan riko a matsayin takura a matsayin rashin sirri a gida saboda duk mace tana so ta ga gidanta daga ita sai ‘ya’yanta shi ne take kallon sa a matsayin sirri, to rashin kallon ‘ya’yan riko a matsayin rashin sirri to wata mata yadda take ganin gidanta akwai sirri, amma a ce akwai dan riko ko dan miji to sai ta ga gidanta ba ta da wani sirri da za ta yi ba ta da wata kariya shike nan nan ma sai ta dauki tsangwama da karan tsana ta dora wa ‘ya’ya ta yi ta azaftarda su.
Hassan Tijjani
Rashin tsoron Allah, da tsantsar munafurci, tare da kisisina da iya Duniyanci, duka har da Zalunci, wasu mata duka suka tattare wadannan abubuwan, a gaban Baban yaro sai kaga mace tana nuna duk duniya babu wanda take so kuma
take tausayi sai wannan yaron, da zarar uban ya futa wani idan aka baki labarin abinda take yiwa wannan yaron wlh kare ma baza ka yiwa irin wannan ba idan akwai Imani, to shi yasa ake samun matsaloli saboda shi uba ga yadda akeyi a gabansa sannan kuma ba haka akeyi a bayan idonsa ba idan wani ya bashi labari bazai yarda ba saboda shi yana ganin yadda akewa yaransa a gabansa.
Amma Matan ba duka aka taru aka zama daya ba akwai masu Imani wadanda baza su iya irin wannan zaluncin ba.
Shawara ga Mata masu irin wannan halin: idan kinsa ba za ki iya adalci a tsakanin yaranki Matanmu.inki wadda wata ta haifa masa to ki auri saurayi karki auri mai mata ko kuma karki auri wanda ya taba aure wato mai ‘ya’ya da wata matar , to ina ga wannan zai dan zama dama dama saboda kinsan dama bashi da kowa a gabansa. Allah ya shirya mana Matanmu
Sumayya Amar
Abubuwan dake jawo wasu mata ke gallazawa yara da aka barmusu amana a hannunsu ko suke rike dasu ba wani abu bane illa rashin amana ko kuma ince cin Amana saboda in har akwai Amana akasari su wadannan mutane basu tsoron Allah kuma basu tunanin mutuwa domin duk wanda zai cutar da yaro to zai iya cutar da kowa domin shi yaro na kowa ne, idan ka taimaki dan wani kamar ka taimaki kanka ne don ba ka san waye zai taimaki naka ba, koda kuwa yaron ba ya ji za ka yi mashi hukunci daidai yadda ya kamata kamar daidai yadda za ka yi wa naka ba na zalunci ko gallazawa ba, mafi akasarin irin wadannan matan jahilai ne shi ne bature ke cewa ‘Educate a woman like you educate the world’.
Hasiya Baba Haruna
To ni a ganina yawancin abin da ke sa mata su gallazawa yara kamar ‘ya’yan mijinsu shi ne wasun su tsantsar zalunci ne, wata idan ka shiga gidan ka ga irin biyayyar da yaran ke yi mata sai sun baka tausayi, amma a haka ma ba su fita ba.
Saboda ta sa wa zuciyarta wani abu can daban, ko na tsakanin su da uwar yaran, maimakon idan ma ramawa za ta yi ta yi akan uwar sai ki ga suna ramawa akan yaran a yi ta gallaza wa yaran, wasu har da uwar yaran za ki ga ana gallazawa shi kuma miji ba shi da katabus bai isa ya ce komai ba saboda an riga an mallake shi sai yadda ta yi a gida.
Wasu kuma za ki ga uwar yaran ba ta gidan kuma kar ki yi mamaki a sanadiyarta uwar ta bar gidan, ta raba ta da ‘ya’yanta sannan kuma take gallaza musu. A yanzu haka akwai wasu mata da sun raba uban da yaran, a cikin gida daya sai ki ga uban sai ya yi sati bai gansu ba kuma bai isa ya tambaya ba, saboda ba su isa su zo inda yake ba, suna daki boye ko kuma suna kicin suna cin uban aiki, daga Asuba ta yi sun shiga kicin su da su fito sai bayan Isha sannan ne za su samu su yi wanka, kuma kar ki ce wai sau daya ne haka kullum ta’alla haka ake a gidan, ka rasa aikin me ake yi, ta dinga kirkiro musu aiki saboda wai ba ta so ta ga sun zauna sun huta ko da na minti biyar ne.
Sannan kuma za ki ga abu kadan suka yi na kuskure sai a hada su da baban ya yi ta musu fada wani ma sharri ne ake yi musu kuma ba su isa su ce ba haka bane, a gaban su za ta fadi karya ita kanta ta san karya take yi musu amma saboda basu isa su ce ba haka bane ta fadi duk abin da za ta fada shi kuma ya dauka ya yi ta musu fada yana zaginsu har ta kai da ya daina yi musu magana.
Sannan ga zalunci da take yi musu idan suka samu kudi ta karbe ta hana su kuma ba za ta saya musu komai ba idan aka ba su wani abu ta karbe ta ba wa ‘ya’yanta ko kuma ita ta yi amfani da shi. Ko uban ya bayar ta saya musu wani abu ba ta saya sai dai ‘ya’yanta ga uban aiki da suke ci.
Abincin gidan da ubansu ya saya su ba’a basu mai dadi, ita da ‘ya’yanta suke ci su kuma a hada su da 247 tuwo.
Sannan idan yanzu za’a yi bako gidan ya ba da abu a raba wa yara to fa su banda su, kuma kar ki yi mamakin duk wani abu da za’a yi na tarbar bakon su suka yi, idan za ki gani mai aikin gidan ta fi su daraja a cikin gidan nasu mai aiki za ta yi yadda take so amma su ba su isa ba. Abin dai babu dadi sai dai Allah ya bamu ikon cikawa da kyau da Imani.