Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin TASKIRA, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne dangane da abin da ya shafi tsafta, musamman maza marasa tsafta, duk da cewa wannan shafi ya sha yin magana a kan wannan batu, sai dai kuma wasu sun bukaci da a kara maimaita batun.
Duba da yadda wasu mazan suke nuna rashin halin ko-in-kula a kansu, tamkar dai wadanda ba su taba ji ko sanin yadda ake yin tsafta ba.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin Taskira gamed a wannan batu; Ko me za a ce a kan maza marasa tsaftace jikinsu?, Me yake janyo hakan?, Me hakan ke iya haifarwa? Ta wacce hanya za a magance afkuwar hakan?.
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Fatima Tanimu Ingawa, Daga Jihar Katsina:
A gaskiya wasu mazan nada kazanta ta yadda ba sa iya tsaftace jikinsu, kama daga tsaftar jiki dana tufafi wanda ya kunshi aski, yanke farce da kuma amfani da turaruka na mai dana kaya. A hakan suke rayuwa da iyalinsu dama al’ummar gari baki daya, wanda hakan bai dace ba domin a kwai cutarwa kwarai da gaske. Abun da ke janyo hakan kuwa rashin kula ne, da kuma wasunsu sun tashi sun saba da rayuwar kazanta. Hanyar da za a magance hakan kuwa shi ne, ta hanyar fadakarwa a kan muhimmancin tsafta da kiwon lafiya. Sannan masu irin wannan hali ya kamata iyalansu su rika kwatanta masu a siyasance, kar suna fita ana jin tashinsu cikin jama’a. Shawara ta a nan shi ne; ya kamata masu irin wannan dabi’a su gyara, su san cewa ita tsafta yanki ne na imani, sannan ita tsafta dadi gare ta ga mai yinta da mai gani da ido. Allah ya basu ikon kiyayewa.
Sunana Hafsat Sa’eed, Daga Jihar Neja:
A gaskiyar magana ana samun hakan da yawa maza masu kazanta, wasu ma ta haka matansu suke koyan kazantar, musamman in daman can suna yi daga baya suka daina, idan suka hadu da namiji mara tsafta sai su koma ‘yar gidan jiya, idan kuwa mace ba ta kazanta to namijin ba karamin cutarta zai ba, sabida ba yadda ta iya da shi ga shi kuma suna tare, dan wani namijin duk hanyar da mace za ta bi dan ya gyaru ba bari yake ba, sai ya rika nuna isa da izza wai shi maigida, dole ta kyale shi a yadda yake, idan me komawa irinsa ce ta koma. Abin da ya ke janyo hakan, daman can mutum a hakan ya ke, yana kallon dan bai tsaftace jikinsa ba hakan ba komai bane. Idan mutum yanada aure yana haifar da matsaloli da dama wajen matarsa, da rashin jituwar da ba zai fahimci ta mece ce ba, sannan kimarsa tana raguwa wajen mutane, da dai sauransu. Haka idan ba shi da aure, ya kan rasa abokai dan kowa zai rika guje masa, kuma ko mace ya ce yana so za ta guje masa ba za ta kaunace shi ba, haka a unguwa yana zuwa waje za a rika watsewa kowa ba zai so a ce abokinsa bane ko yana tare da shi. Namiji ya rika daurewa koda a zuciyarsa baya jin yana so ya tsaftace jikinsa, ya daure ya yi, yana tashi daga bacci ya samu yayi wanka duk wajen daya kamata ya tsaftace dan Allah ya tsaftace koda ya ji dadin jikinsa da kuma farantawa matarsa, ya saka kaya masu tsafta kar ya saka kayan da suka sha rana a jikinsa na jiya ya kara maimaita su, ya samu kaya wankakku ya saka, haka wanki ma ya daure ya rika yi ko ya bayar a yi masa ba sai sun taru ba, hakan zai taimaka masa. Shawara maza a rika tsafta dan Allah dan Annabi, kar ka ga kai namiji ne ba mace ba ka ce kai ba sai ka yi wanka ka shirya ba.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar Kano, Rano:
Wasu a harkar neman abincinsu ne, wasu kuma halittarsu ce a haka gani suke tunda kullum suna waje wajen nema ba dole su yi tsafta ba. Rashin sanin mutuncin kai ga wasu mazan wasu kuma kawai sun bari matane ‘yan kwalliya basu san cewa su ma matan suna son ganin namiji cikin tsafta ba. Ya kan kawo raini ga matansu da kuma ‘yan matansu d.s. Wannan kuma idan namiji mai wannan dabi’ar yana da aure nauyin yana kan matarsa ita ta san dabarun da za ta yi wajen ankarar da shi hakan. Idan saurayi ne nauyin ya hau kan budurwarta sa idan har tana sonsa. Shawarata a nan ita ce; gaskiya muna yin tsafta duba da tsafta ma tana daga cikin addininmu na islama sannan za mu ji dadin jikinmu, sannan kamar yadda muke son ganin yaranmu matanmu ‘yan matanmu cikin shiga da tsafta da kamala to haka su ma suna son su ganmu a hakan. Allah ya sa mu dace amin.
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:
Hakika a kwai mazaje da dama masu irin wannan hali, kuma hakan sam-sam bai dace ba, domin tsafta aba ce mai matukar muhimmanci a fannin addinin musulunci da dama mu’amula da al’umma don haka ya zama wajibi mutum ya ke kula da tsaftacce duk kanin sassan jikinsa da ma suturarsa. To abun da ya ke jawo haka magana ta gaskiya sakaci ne na mutum domin babu wani dalili da zai sa mutum ya ki tsaftacce jikinsa, koda kuwa babu wadata ko a ce karamin karfi domin ita tsafta ita ce kula da jiki ba wai yawan sa sabon kaya ba, gyara jikin shi ne tsafta, ka ga kuwa babu dalilin da zai sa mutum ba zai ke ware lokaci yana tsaftacce jikinsa. To masu irin wannan hali suna cutar da iyalansu da sauran al’ummar dake mu’amula da su, kuma suna cutar da kansu da kuma tauye ibadar su da suke gudanarwa a yau da kullum. To hanyar da za a bi ita ce; a basu shawara cikin hikima da kuma dabara domin su gane muhimmanci tsaftacce jikinsu a fannin gudanar da addinin musulunci da kuma mu’amula da iyalansu da al’ummar da suke mu’amula da su. To shawara ta a nan ita ce; ya kamata su sani tsaftacce jiki wajibi ne ba wai ra’ayi bane muddun suna so idan sun yi ibadar su ta karbu dari bisa dari, kuma hakan zai taimaka wajen su daina cutar da iyalansu dama al’ummar da suke mu’amula da su, daga karshe hakan zai taimaka wajen inganta lafiyar jiki dama mu’amula a tsakanin al’umma.
Sunana Mansur Usman Sufi (Sarkin Marubutan Yaki) Daga Jihar Kano:
Maganar gaskiya ina matukar takaici na ga namiji kazami ba tsafta, kuma abun bacin rai ne. Gaskiya abin da ke kawo hakan jahilci ne da rashin darajar kai, domin ba za ka taba ganin mai ilimi kazami ba. Abin da kuma rashin tsafta zai haifarwa mutum shi ne zubewar Æ™ima da daraja a idanun al’umma. Hanyar da za a magance hakan yin nasiha ga wanda ya yake aikatawa ya kuma gane cewa hakan ba addini ba ne. Shawarata ga masu aikata hakan shi ne; su gyara domin Allah mai Tsarki ne baya karbar aiki sai mai tsarki
Sunana Salma Nasir Adam, Daga Jihar Katsina:
Zancen gaskiya ana samu sosai ma, dan wani namijin sai ka ganshi ya sha kaya masu kyau daga nesa yana matsowa kusa da kai za ka ji kamshi daban wari daban, ya yi ta bugawa wallahi, sai ka ji da ma bai saka kayan daya saka ba, sabida ba su dace da jikinsa ba. Ka kan rasa gane rashin tsaftar namiji, in ka ci karo da mara tsafta ko’ina na jikinsa babu safta koda kuwa kayan da yake sakawa masu kyau ne, yana bude bakinsa sai ka ji wari, wani in Allah ya hada ku cikin abin hawa wajen tafiya har ka sauka bakinka a kunshe sabida warin da ke tashi a jikinsa, kuma shi ko a jikinsa. Dan Allah maza a rika tsafta kodan shiga cikin mutane da kuma yin ibada ingantacciya, dan wallahi hakan ba karamin zubar da kima da mutunci bane, idan mutum.yanada tsafta kowa sonshi yake yi komai muninsa, amma in mutum ba shi da tsafta kowa kyamarsa ya ke komai kyansa.