• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Najeriya Za Ta Iya Samu Daga Tsarin BRICS?

byCGTN Hausa and Sulaiman
12 months ago
Brics

Ana ci gaba da gudanar da taron ganawa tsakanin shugabannin kasashe mambobin BRICS a birnin Kazan na kasar Rasha yanzu. A nata bangare, kasar Najeriya ta bayyana niyyarta ta shiga cikin tsarin BRICS har sau da dama. Na tuna a taron FOCAC da ya gudana a Beijing na Sin a watan Satumba da ya gabata, Yusuf Tuggar, ministan harkokin wajen kasar Najeriya ya ce, “Ba wanda zai iya hana Najeriya shiga cikin tsarin BRICS, ganin yadda kasar ta girma, kuma ta iya yanke shawara da ita kanta kan wane ne za ta yi hadin gwiwa.” 

 

Sai dai me tsarin BRICS zai haifarwa Najeriya, idan ta shiga cikin tsarin? Za mu iya samun amsa dangane da tambayar, cikin jawabin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi a taron kolin BRICS na wannan karo.

  • Sojoji Sun Ceto Mata 3, Sun Kwato Makamai A Katsina Da Zamfara
  • Tsarin BRICS Na Samun Karin Karbuwar Kasashe Daban-Daban

Jawabin shugaba Xi ya nuna alkiblar da tsarin BRICS ya dosa, da matsaya daya da mahalarta taron BRICS na wannan karo suka cimma, wanda ya kunshi wasu kalmomi masu muhimmanci, wato su: zaman lafiya, da ci gaba, da hadin gwiwa, da adalci, da kirkiro sabbin fasahohi, da kare muhalli, gami da cudanyar al’adu.

 

LABARAI MASU NASABA

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang

Da farko dai, yadda aka jaddada muhimmancin zaman lafiya, ya nuna cewa, kasashe mambobin BRICS sun fi son tattaunawa maimakon fada. Saboda haka, idan kasar Najeriya ta samu damar shiga cikin tsarin BRICS, to, ba ya nufi ta dauki wani bangare don takara ko fada da wasu. Maimakon haka, za ta samu karin damammakin hadin kai don tabbatar da tsaronta, da na yankin da take ciki.

 

Na biyu shi ne, batun ci gaban tattalin arziki. Ta yaya tsarin BRICS zai iya taimakawa kasashe masu tasowa wajen samun ci gaba mai dorewa? Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana ayyukan da kasar Sin ta yi a wannan fanni, misali kafa cibiyar raya fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI, ta Sin da BRICS, da habaka hadin gwiwar da take yi tare da sauran mambobin BRICS ta fuskar masana’antu mai nasaba da fasahohin kare muhalli, da dai sauransu. Saboda haka, idan Najeriya ta shiga cikin tsarin hadin kai na BRICS, to, za ta samu damar raya wadannan bangarori, tare da inganta tsarin masana’antu a cikin gida.

 

Bangare na uku ya shafi hadin gwiwar kasashe mambobin BRICS, wadda ta kasance karkashin tsarin hadin kai na daukacin kasashe masu tasowa. Ta hanyar hada karfin wadannan kasashe, za a iya daidaita tsarin kula da al’amuran kasa da kasa, don ya zama mai adalci.

 

Hakika kasashe mambobin BRICS suna da karfin tattalin arziki. Yanzu yawan GDP nasu ya kai kashi 36% na GDPn daukacin duniya, yayin da GDPn rukunin G7 da wasu manyan kasashe dake yammacin duniya, irinsu Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Jamus, suka kafa, bai wuce kashi 30% na adadin duniya ba. Sa’an nan idan an binciki bangaren karuwar tattalin arziki, za a ga karuwar GDPn kasashen BRICS za ta kai kashi 4% a bana, da ta fi kashi 1.7% ta rukunin G7.

 

Yanzu haka, bisa karfinsu na fannin tattalin arziki, kasashe mambobin BRICS na kokarin samar da damammaki ga kasashe masu tasowa, don su fitar da kansu daga kangin da kasashen yamma suka saka su, da niyyar kare ikonsu na yin babakere a duniya. Saboda haka, shugaba Xi ya jaddada a cikin jawabinsa bukatar baiwa kasashe masu tasowa karin wakilci a hukumomin kasa da kasa, da damar tofa albarkacin bakinsu kan al’amuran duniya, gami da daidaita tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa.

 

A nata bangare, kasar Najeriya ta sha wahalhalu sakamakon sauyawar darajar dalar Amurka, inda take bukatar gyare-gyare kan tsarin hada-hadar kudi na duniya. A sa’i daya kuma, kasar, bisa matsayinta na babbar kasa mai dimbin al’umma da karfin tattalin arziki a Afirka, na neman damar zama mai fada a ji a hukumomin kasa da kasa daban daban. Ta haka za mu iya ganin cewa bukatun kasar Najeriya da burin tsarin BRICS daya ne.

 

Sa’an nan a bangare na karshe, wanda shi ma yana da matukar muhimmanci, za mu ambaci cudanya a fannin al’adu. A cewar shugaba Xi na kasar Sin, ya kamata a tabbatar da kasancewar mabambantan al’adu a duniyarmu, da hakuri da juna, da koyi da juna a tsakaninsu. Ta haka ake neman daidaita tsarin da kasashen yamma suka kafa na nuna girman kai a fannin tunani da na al’adu, don baiwa kasashe daban daban damar samun ‘yancin tunani, da neman hanyar raya kai da ta dace da al’adunsu. A Najeriya, al’adun kasashen yamma da tsarinsu na mulki, da ‘yan mulkin mallaka suka kawo wa kasar, sun haifar da cikas ga yanayin samun ci gaban al’adun kai a kasar, tare da haddasa dimbin matsalolin dake damun kasar har zuwa yanzu. Don neman daidaita matsalolin daga asali, da samun dabarar raya kai da ta dace da al’adun kanta, Najeriya za ta iya aiwatar da karin cudanya tare da kasashe mambobin BRICS.

 

Idan mun takaita bayanin dake sama, za mu san cewa, shiga cikin tsarin BRICS na nufin tsaro, da ci gaban tattalin arziki, da yin tasiri a fannin al’amuran kasa da kasa, da samun ‘yancin tunani, ga kasar Najeriya. Wannan nau’in alfanu shi ma ya sa tsarin BRICS ke janyo hankalin dimbin kasashe masu tasowa a kai a kai. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka
Ra'ayi Riga

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang
Ra'ayi Riga

Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang

September 30, 2025
Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka

September 29, 2025
Next Post
Xi Ya Halarci Taron Tattaunawa Na Jagororin “BRICS+” Tare Da Gabatar Da Muhimmin Jawabi

Xi Ya Halarci Taron Tattaunawa Na Jagororin "BRICS+" Tare Da Gabatar Da Muhimmin Jawabi

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version