Tun daga watan Maris na shekarar bana, kasar Philippines ta kara tada zaune tsaye a yankin kewayen sashen tudun ruwa dake kudancin tekun kasar Sin. A ranar 5 ga wannan wata, kasar Philippines ta aike da jiragaren ruwan dakon kaya biyu, da na dakarun tsaron teku biyu zuwa yankin teku dake dab da sashen tudun ruwa na Ren’aijiao, tare da yin karo da jiragen ruwan sojan Sin da gangan. Bayan kwanaki 18 kawai, bangaren kasar Philippines ya keta alkawarin da ya yi, ya sake aikewa da jirgin ruwan dakon kaya daya, da na dakarun tsaron teku biyu, ba tare da amincewar bangaren kasar Sin ba, zuwa sashen tudun ruwa na Ren’aijiao.
Manazarta sun yi nuni da cewa, bangaren kasar Philippines yana ta yunkuri a fannoni uku bisa matakan da ya dauka a tekun kudancin kasar Sin. Na farko dai, yana son lalata mutuncin kasar Sin a duniya ta hanyar tada zaune tsaye ta hanyar nanata matsayinta kan kudancin tekun Sin. Na biyu, ya ci gaba da hura wutar rikici a kudancin tekun Sin, don neman dalilin da zai baiwa bangaren Amurka damar tsoma baki kan harkokin yankin. Na uku kuwa, kasar Amurka, da Japan, da ta Philippines, za su gudanar da taron koli a birnin Washington dake kasar Amurka a watan Afrilu, don haka matakan Philippines za su samar da karin hujojin da za a iya tattauna a kansu a gun taron kolin.
- Sin Ta Zamo Ta Daya A Yawan Jarin Waje Da Ake Zubawa A Tanzania
- Zhao Leji: Zuba Jari A Sin Zuba Jari Ne Don Gaba
Kowa ya san cewa an tabbatar da ikon mallakar yankunan Sin, da moriyar tekun kasar a dogon tarihi, kana suna dacewa da dokokin kasa da kasa, kamar su kundin tsarin mulkin MDD, da yarjejeniyar dokar teku ta MDD da sauransu. Kana an tabbatar da iyakar yankin kasar Philippines bisa jerin dokokin kasa da kasa, amma hakan bai shafi dukkanin tsibiran Nansha ba. Amma kasar Philippines ta ci gaba da aikawa da jiragen ruwa zuwa yankin tekun kasar Sin ba bisa doka ba, lamarin da ya keta ikon mallakar yankunan kasar Sin da moriyar tekun kasar.
Dukkanin wadannan na shaida cewa, kawancen Amurka da Philippines ya haifarwa yankin yanayi na tada zaune tsaye, ba wai zaman lafiya ba. (Zainab Zhang)