Abokai, Panda wata dabba ce dake da tarihi na a kalla shekaru miliyan 8 a duniya, kuma dabba ce dake fuskantar barazanar karewa baki daya daga doron kasa, hakan ya sa aka sanya ta cikin dabbobin da ake iyakacin kokarin kare su. Dabbobin Panda na rayuwa ne a dajin kasar Sin kawai. Amma saboda yadda al’ummar sauran kasashe ke matukar son Panda, gwamnatin kasar Sin ta fara bayar da aron Panda zuwa kasashen da suka cancanci ba da kulawa gare su, shi ya sa Panda ta zama dabbar dake alamanta zumunci.
Amma halin da Panda da Amurka ta ara dake gidan dabbobi na Memphis ke ciki ba shi da kyau, abin da ya fusata mutane sosai. A watan Disamba na bara, wannan gidan dabbobi ya sanar da maido da Panda biyu ga kasar Sin saboda wa’adin shekaru 20 na kwangilar aron ta kare. Amma abin bakin ciki shi ne, wata Panda mai suna “LE LE” ta mutu sakamakon ciwon zuciya a watan da ya gabata. Dayar mai suna “Ya Ya” ita ma ba ta cikin hali mai kyau. Sabo da idan Panda tana da lafiya, za a ga tana da kiba kamar siffar kwallo, amma “Ya Ya” yanzu tana fama da ciwon fata har gashin jikinta ya zube, rashin abinci mai inganci, ya sa ta rame.
Tabbatar da lafiyar jikin Panda wani muhimmin abu ne dake cikin kwangilar aron Panda da Sin ta kulla da kasashen da suke son aronta. Ban da wannan kuma, dokar tabbatar da hakkin dabobbi da Amurka ta zartas da ita a shekarar 1980, ta tanadi cewa, ya kamata a tabbatar da hakkin dabbobi, ciki hadda ba su kulawa yadda ya kamata da hana cin zarafinsu. Amma Panda a matsayinta na dabbar dake alamanta zumunci, ba a kula da ita sosai ba a gidan dabbobi na Memphis na Amurka, abin da ya fusata duk wani mai son Panda. Ko hakkin dabobbi Amurka ba ta iya kare ba, balle hakkin Bil Adama.
A hanzarta maido da “Ya Ya” gida nan kasar Sin, ta yadda za a ba ta kulawar da ta dace. (Mai zana da rubuta: MINA)