• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Amare Ke Son A Nuna Musu Fifiko Kan Uwargida?

by Amina Usman
3 years ago
Amare

Mafi akasari wannan ita ce matsalar da ta addabi gidajen aure musamman a yankin Arewacin Nijeriya.

In muka duba za mu ga cewa wannan matsalar tana faruwa ne daga bangaren maigida domin kuwa tun a wurin neman auren zai baje wa amarya dukkan irin hidimar da ake yi a gidansa kama daga yadda suffar uwargida take har zuwa yadda take gudanar da ala’amuranta a cikin gida.

  • Gajartar Amarya Tasa Ango Ya Fasa Auren Amaryarsa Ana Tsaka Da Gudanar Da Biki

A lokacin da yawanci maza suke neman aure su kan dukanta da irin romon soyayya da suke samu daga wurin yarinyar da suke nema, har ta kai ga za ka ga ana kokarin raba kwanaki tsakanin uwargida da kuma yarinyar da za a auro.

Da wadannan halaye ne maza suke sayar da mutuncin uwargida a waje wanda hakan zai ba wa ita amaryar da za a auro lasisin cewa fa ashe ma ‘matar gidan ba ta da fada a gidan, mijin baya son ta ni ya fi so, ko kuma ta ji a ranta cewa ita ce ‘yar gaban goshi ‘ da ire-iren wannan tunanin ne yawanci amare suke shiga gidajen aure.

Wanda tun a waje ta gama daura damarar cewa in ta shigo ita ce ‘yar gaban goshin miji saboda haka babu sauki tsakaninta da uwargida.
Bayan aure sai ka ga amarya ta dauki tsirfa iri-iri wai ita dole sai ta chusa wa uwargida bakin ciki, uwar gidan da ta yi shekara goma da miji sai ka ga yarinya karama an auro ta ta zo tana kokarin nunawa uwargida cewa fa ta fita sanin miji.
Da yawa amare suna shiga cikin gidajen aurene da niyyar uwargida tafita ta bar musu mijin domin ita ba ta iya kula da miji ba su ne suka iya soyayya su ne suka iya kula da miji.
Uwargida tana fuskantar hali da dabi’u iri daban -daban a wurin amarya wanda hakan ya samo asali ne daga irin tadin da shi mijin ya yi wa amarya tun a wurin neman auren ta.
Wani mijin tsabar dadi soyayya zai gama zayyana duk irin zaman da suke yi da uwargida mai dadi ko mara dadi inda su kuma amaren suke riko da shi a matsayin makamin muzgunawa uwargida, tun da burin kowace amarya shi ne miji ya fi son ta, laifin uwargida kadan ake jira har da wanda ba ta yi ba a kai kara wurin miji, shi kuma dama dadi amarya ba zai bar shi ya yi bincike ba zai hau fada yana masifa, wanda hakan kan haifar da rashin jituwa a tsakani.
Ko hira ake yi sai ka ga amarya na kokarin nuna wa uwargida ai ta fi ta sanin kan miji, a dole sai ta nunawa uwargida ita ce fa yar gaban goshin miji.
Mazaje su suke da babban kaso a irin halayen da amare ke shigowa da su gidaje.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

Hadin Tsumin Baure

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Hadin Tsumin Baure
Ado Da Kwalliya

Hadin Tsumin Baure

September 27, 2025
Gyaran fuska
Ado Da Kwalliya

Gyaran Fuska Da Laushin Fata

August 30, 2025
Next Post
Wang Yi Ya Yi Fashin Baki Game Da Tasirin Ziyarar Shugaba Xi A Gabas Ta Tsakiya

Wang Yi Ya Yi Fashin Baki Game Da Tasirin Ziyarar Shugaba Xi A Gabas Ta Tsakiya

LABARAI MASU NASABA

Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Amare

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

October 27, 2025
Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

October 27, 2025
Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

October 27, 2025
Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.