A daidai lokacin da kasashen duniya ke yin Allah wadai da yadda gwamnatin kasar Japan ta kare aniyarta ta zubar da ruwan dagwalon nukiliya na tashar nukiliya ta Fukushima cikin teku, jakadan kasar Amurka a Japan Rahm Emanuel ya yi tattaki zuwa Fukushima, inda ya nuna yadda ya ci abincin teku na wurin, don bayyana goyon baya ga matakin da Japan ta dauka na zubar da ruwan cikin teku. Amma da gaske ne Amurka ba ta damu da illolin da matakin na Japan ka iya haifarwa?
Alkaluman da ma’aikatar kula da aikin gona da dazuzzuka da albarkatun ruwa ta kasar Japan ta fitar sun shaida cewa, Amurka ta kasance kasar da ta fi yawan rage shigowa da kayayyakin ruwa daga kasar Japan tun farkon bana, musamman ma wasu nau’o’in abincin teku da suka fito daga yankin da ruwan dagwalon nukiliya ya fi shafa. Da haka, muna iya gano cewa, gwamnatin Amurka na sane da illolin da matakin ka iya haifarwa. To, ke nan me ya sa Amurka ta nuna hakuri har ma ta goyi bayan Japan ?
A hakika, matsayin da Amurka ke dauka kamar ciniki ne take yi da Japan, inda ta hanyar bayyana goyon baya da fahimta, Amurka ke taimakawa Japan wajen tinkarar kyama da shakku da ake nuna mata, yayin da Japan a nata bangare, ta kara ba Amurka hadin kai wajen aiwatar da shirye-shiryenta a duniya. A hakika, a cikin shekaru biyu da suka wuce, Japan ta yi ta kokarin ba da hadin kai wajen aiwatar da tsarin tattalin arziki a kasashen dake yankin tekun Indiya da fasifik wato Indo-Pacific da Amurka ke jagoranta.
Amurka wadda a kullum ke ikirarin mai rajin kare muhalli, amma ainihin abin da take kulawa ba muhallin duniya ba ne, illa ci gaba da yin babakere a duniya.
Makonni biyu ke nan da Japan ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku, kuma hakan zai ci gaba nan da shekaru 30 zuwa 40 masu zuwa. Wani nazarin da jami’ar Tsinghua ta kasar Sin ta yi ya shaida cewa, da farkon fari, kasashen da ke yammacin tekun Pasifik ne za su fi fuskantar illolin da matakin zai haifar, amma sakamakon igiyar ruwa, nan da shekaru 10 masu zuwa, yankin Amurka da ke gabashin tekun za su fuskanci tarin sinadarai masu guba da suka ninka na mashigin teku na Japan har sau uku.
Abin takaici shi ne, ‘yan siyasa na Amurka sun fi mai da hankali a kan cimma moriyarsu ta yanzu, babu ruwansu da matsaloli da gwamnati ta gaba za ta fuskanta. (Mai zane: Mustapha Bulama)