“Me ya sa kasar Sin ba za ta bar Taiwan samun ‘yancin kai ba?” Wani ma’aikacin banki ya yi mana wannan tambaya, yayin da nake kula da wasu ayyuka a wani banki dake Lagos na Najeriya, wasu shekaru da suka wuce. Sa’an nan, na mayar masa da wata tambaya ta daban, wato “Me ya sa tarayyar Najeriya ba ta ba Biafra damar samun ‘yancin kanta ba?”
Da ma’aikacin ya ji wannan tambayar, sai ya yi murmurshi, ya kuma cewa abokin aikinsa, “Ga wannan mutum da ya san tarihinmu.”
- Ko Barcelona Ta Kama Hanyar Lashe Gasar Laliga Ta Bana?
- Yunkurin Neman ‘Yancin Kan Taiwan Ya Shaida Yunkurin Lai Ching-te Na Neman Mulki Irin Na Kama Karya Ta Hanyar Demokuradiyya
Duk wani lokaci da wani aboki ya tambaye ni kan batun Taiwan, na kan gaya masa cewa, idan mun bayyana batun bisa wani tsari a takaice, to, yankin Taiwan ga kasar Sin, tamkar yankin kudu maso gabashin Najeriya a karkashin ikon Biafra ga tarayyar Najeriya. Najeriya ta jure yakin basasa na shekaru 3, da mutuwar mutane kimanin miliyan 1, wajen hana ballewar yankin kudu maso gabas. Hakazalika kasar Sin ita ma a nata bangare, tana da irin wannan niyya mai karfi, don tabbatar da dinkuwar kasa.
Ko da yake sanin tushen batun Taiwan ba shi da sarkakiya, amma a kan iya ganin kuskure cikin bayanan da kafofin watsa labaru na Najeriya suka gabatar dangane da batun. Misali, a kwanan baya, jaridar Premium Times ta ruwaito maganar da Andy Yih-Ping Liu, shugaban ofishin harkar ciniki na Taipei, ya fada, inda ya zargi gwamnatin Najeriya da “bin umarnin kasar Sin”, bisa bukatar hukumar Taiwan da ta janye ofishinta daga birnin Abuja zuwa Lagos, da sake nada masa suna “ofishin harkar ciniki na Taipei”. Sai dai maganar gaskiya ita ce, manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, (wadda ta kunshi bangarori uku: 1. Akwai kasar Sin daya tak a duniya. 2. Taiwan wani yanki na kasar Sin ne da ba za a iya balle shi daga kasar ba. 3. Gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin ita ce halastacciyar gwamnati daya tak dake wakiltar daukacin yankunan kasar Sin.) ita ce tushen kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin. Saboda haka, yadda Najeriya take da huldar diplomasiyya da kasar Sin, ya nuna yadda kasar take yarda da manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. To, hakan zai hana gwamnatin Najeriya baiwa yankin Taiwan damar kafa ofishi a Abuja, wadda take ba wa kasashe masu ‘yancin kai kawai. Ta haka ma za a fahimta cewa, matakin da Najeriya ta dauka cika alkawari ne, maimakon bin umarnin wani.
Ban da haka, a cikin bayanin jaridar Premium Times, an ce “Bayan da aka kawo karshen yakin basasa a kasar Sin a shekarar 1949, jam’iyyar KMT ta tsira zuwa Taiwan, inda ta kafa jamhuriyar kasar Sin.” To, wannan maganar ita ma ba haka take ba. Maganar gaskiya ita ce, an kafa jamhuriyar kasar Sin tun shekarar 1912, wadda ta kunshi harabar babban yankin kasar Sin, da ta yankin Taiwan, na yanzu. Sa’an nan a sakamakon kammalar yakin basasa a shekarar 1949, gwamnatin tsakiya na jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta kafu, wadda ta maye gurbin gwamnatin jamhuriyar kasar Sin a matsayin halastacciyar gwamnati daya tak ta daukacin yankunan kasar Sin, da halastacciyar wakiliya ta kasar Sin guda daya tak a duniya. Lamarin da ya kawo karshen jamhuriyar kasar Sin a lokacin.
Sai dai hukumar yankin Taiwan na ci gaba da kokarin yada karairayi, tare da tunasar da kowa kasancewarta. In ba haka ba, wadannan bayanai masu kunshe da kurakurai da muka ambata ba za su bayyana a kan wata jaridar Najeriya ba. Hakika, a shekarun nan, hukumar Taiwan ta yi ta kokarin takala da batun neman “‘yancin kan Taiwan”, lamarin da ya haifar da mummunar barazana ga zaman lafiyar shiyyar da yankin ke ciki. Kamar ba su cika lura da dokar kin barakar kasa ta kasar Sin, wadda aka fara aiwatar da ita wasu shekaru 20 da suka wuce ba. Sai dai an tanada a cikin dokar da cewa, babban yankin kasar Sin zai nuna cikakken sahihanci, da iyakacin kokarin tabbatar da dinkuwar kasa ta hanyar lumana, amma zai dauki kwararran matakan da suka wajaba, idan masu neman “‘yancin kan Taiwan” sun wuce gona da iri.
Tabbas za a tabbatar da dinkuwar kasar Sin waje guda. Yadda masu neman balle yankin Taiwan ke ta da zaune-tsaye ba zai haifar musu da da mai ido ba, illa sanya su gamuwa da ajalinsu cikin sauri. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp