• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa BRICS Ke Kara Samun Karbuwa Daga Kasashen Duniya

by CMG Hausa
2 years ago
BRICS

“Kasashen BRICS na kasance tamkar maganadiso, wanda ke ta jawo masu neman tabbatar da zaman lafiya da hadin gwiwa… Mu ma Venezuala, muna fatan zama daya daga cikin kasashe mambobin BRICS.”

Shugaban kasar ta Venezuala Nicolás Maduro Moros ne ya fadi haka a kwanan baya a gun taron manema labarai da aka shirya bayan ganawarsa da takwaransa na kasar Brazil.

  • Jami’in Afirka Ta Kudu: Jagororin Dukkan Kasashen BRICS Za Su Halarci Taron Kolin BRICS Din Na Bana

Daga ranar 1 zuwa 2 ga wata, an gudanar da taron ministocin wajen kasashen BRICS a birnin Cape Town na kasar Afirka ta kudu, kuma fadada mambobin kungiyar na daya daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna a gun taron.

Bayanai na cewa, kasashe da dama ciki har da kasashen Afirka irinsu Aljeriya da Masar, duk sun bayyana burinsu na zama mambobin kungiyar BRICS, kafin wannan kuma, wakilin musamman na gwamnatin kasar Afirka ta kudu mai kula da harkokin Asiya da gabas ta tsakiya da kuma kasashen BRICS, Anil Sooklal ya bayyana cewa, “Kusan muna samun sakwannin neman zama mambar BRICS a kowace rana.”
Amma me ya sa BRICS ke kara farin jini?
In mun yi nazari, za mu gano cewa, hakan ya faru ne sabo da na farko, kungiyar BRICS na jawo hankalinsu ne sabo da yadda take neman hadin gwiwa da ci gaba, a maimakon rarrabuwar kawuna da yin fito na fito da juna.

Ba kamar yadda Amurka da kawayenta na yammacin duniya su kan kulla kawance ne don su tinkari wani, tsarin BRICS tun farkon kafuwarsa yana mai da hankali ne a kan inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa. A sa’i daya kuma, ba ya da niyyar yin fito na fito da kasashen yamma ko kuma maye gurbinsu.

LABARAI MASU NASABA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Na biyu kuma, kasashen BRICS na dukufa a kan daidaita tsarin gudanar da harkokin duniya da ma kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, sakamakon yadda kasashe masu tasowa ke fuskantar karancin wakilci da ma jin muryarsu a harkokin duniya. Tun kafa shi, tsarin na BRICS ya yi ta kokarin fito da muryar kasashe masu tasowa a duniya da kuma kare moriyarsu ta bai daya.

In mun dauki misali da asusun ba da lamuni na duniya(IMF), wanda kasancewarsa muhimmiyar hukumar kula da hada-hadar kudi ta duniya, amma kuma ta dade tana wakiltar kasashen yamma ne kawai.

Sai dai bisa kwaskwarima da aka sha yiwa asusun, tsarin BRICS ya kyautata wakilcin kasashe da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa a hukumar ta IMF.

A gun taron ministocin wajen BRICS da aka gudanar a wannan karo kuma, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Ma Zhaoxu ma ya sake jaddada cewa, ya kamata a kara wakilcin kasashe masu tasowa tare da kara jin muryarsu a harkokin duniya.

Na uku, BRICS na mai da hankali ne a kan cimma hakikanan nasarori da za su amfanawa kasashe masu tasowa.

In mun dauki misali da bankin NDB da kasashen BRICS suka kafa, wanda ya kasance banki na tsakanin kasa da kasa na farko da kasashe masu tasowa suka kafa, wanda tun kafuwarsa a shekaru 7 da suka wuce har zuwa yanzu, rancen kudin da ya samar har ya kai dala biliyan 32, wanda aka zuba su a fannonin bunkasa ababen more rayuwa da ma wasu ayyuka na tabbatar da dauwamammen ci gaba a kasashen BRICS.

Musamman ma a lokacin da aka fuskanci annobar Covid-19, Bankin ya samar da kudin agajin gaggawa na dala biliyan 10 ga kasashe mambobin BRICS.

Yadda karin kasashe ke neman zama mambobin BRICS ya shaida mana bukatu na bai daya na kasashe masu tasowa, wato yin hadin gwiwa da juna don tabbatar da bunkasuwar juna, da kara tabbatar da adalcin tsarin duniya.(Lubabatu Lei)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
Next Post
Ana Bin Jihar Kano Bashin Sama Da Naira Biliyan 240, Inji Abba Gida-gida 

Gwamna Yusuf Ya Kori Jami’an Cibiyar Alhazan Kananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

LABARAI MASU NASABA

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025
Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.