Tun daga farkon wannan mako, Beijing, babban birnin kasar Sin ya fara karbar baki daga kasashen Afrika da suka hada da shugabannin kasashe da gwamnatoci da ma manyan jami’ai, da suka zo domin halartar taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen nahiyar Afrika wato FOCAC. A bana, Beijing zai sake ganin haduwar shugabannin bangarorin biyu, bayan wanda aka yi a shekarar 2018.
Dandalin FOCAC dai ya zama wata laima da hadin gwiwar Sin da Afrika ke fadada karkashinsa, duba da irin alfanun da yake tattare da shi. Tun bayan kafuwarsa shekaru 25 da suka gabata, har kullum dandalin na nacewa ne ga ka’idojin gudanar da tsare-tsare tare, samun ci gaba tare da ma moriyar juna tsakanin bangarorin biyu.
- An Gudanar Da Taron Ministoci Na Dandalin FOCAC Karo Na 9 A Beijing
- NNPC Ya Ƙara Farashin Man Fetur Zuwa 855 Kan Kowace Lita
Me ya sa dandalin da ma dangantakar Sin da Afrika ke samun karbuwa?
A duk lokacin da aka ambaci kasar Sin, ba shakka abun da zai zo ran al’ummar Afrika shi ne, taimakon kasar gare su. Tabbas kasar Sin ta zama aminiya ta kwarai mai taimako ba tare da la’akari da ana cikin wuya ko dadi ba, kana ba tare da wani sharadi ko yin katsalandan cikin harkokin gidan kasashen Afrika ba. Taimakon kasar Sin ya isa lungu da sako da kowanne bangare na Afrika. Kama daga ababen more rayuwa zuwa kiwon lafiya da tallafin ilimi da cinikayya da horo da abinci da sauransu.
Na yi imani a cikin lokacin da aka dauka ana hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, ta samar da taimako na zahiri da manyan kasashe masu mulkin mallaka ba su samar ba, tsawon lokacin da suka dauka suna mamaya a nahiyar Afrika.
Hausawa kan ce, ruwan da ya dauke ka, shi ne ruwa. Ina da yakinin babu wani mutum daga nahiyar Afrika da bai ci moriyar wani abu daga kasar Sin ba. Jama’ar Afrika, sun gani kuma sun shaida huldar Sin da kasashensu, sun kuma ga alfanunta a zahiri, shi ya sa kasar Sin ke kara samun karbuwa a wajensu. (Fa’iza Mustapha)