ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Dangantaka Da Sin Ke Samun Karbuwa A Afrika?

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

Baki sama da 300 daga Sin da kasashen Afrika 53 ne suka tattauna a jiya Litinin game da gudanar da taron dandalin FOCAC na badi.  

Dandalin FOCAC dai ya kasance muhimmiyar laima da kasashen Sin da Afrika ke hadin gwiwa karkashinta, wanda kuma ke samun karbuwa matuka tsakanin kasashen Afrika. Shin me ya sa dangantaka da Sin ke kara samun karbuwa a Afrika?

  • Sin Na Fatan Za’a Daidaita Batun Palestinu Daga Dukkan Fannoni Kuma Na Dogon Lokaci
  • Bikin Ranar Majalisar Dinkin Duniya: Muna Fuskantar Kalubalen Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba – Schmale

Saboda kasar Sin ta zo da sabuwar dabarar hadin gwiwa da ba a saba gani ba. Wato mutuntawa da girmawawa da moriyar juna. A baya, hadin gwiwa da kasashen Afrika ke yi da iyayen gidansu, ta kasnace bisa wasu sharudda da wadancan kasashe ke gindayawa ko kuma ci da gumin kasashen da kwashe albarkatunsu. Amma a yanzu, ba haka abun yake ba, kasashen Afrika sun san darajar kansu saboda yadda kasar Sin ke daukarsu a matsayin ’yan uwanta ba tare da nuna iko ko fifiko ba.

ADVERTISEMENT

Abu na biyu shi ne, kasar Sin tana fada da cikawa. Wato tana samar da tarin damarmaki tare da cika alkawuranta. Na yi imanin cewa, irin alfanun da kasashen suka samu daga hadin gwiwarsu da Sin a kankanin lokaci, bai kai abun da suka samu daga iyayen gidansu masu mulkin mallaka ba. Babu inda kasar Sin ba ta taba ba a fannonin rayuwar al’umma, kama daga ababen more rayuwa zuwa tsaro da kasuwanci da fasahohi da sauransu. Ba za a iya taba raba ci gaban da kasashen Afrika suka samu cikin sauri ba da taimakon kasar Sin.

Abu na 3 a ganina shi ne, yadda kasar Sin ta samarwa kasashen Afrika damar bayyana ra’ayinsu. Bisa yadda take tafiyar da dangantakarta da su, yanzu kasashen Afrika sun san abun da ya dace da su, da yadda za su kwaci kansu. Yayin wani taro da aka gudanar tsakanin kasashen Afrika da na Turai a kwanakin baya, na ji shugaban wata kasa a Afrika na cewa, lallai ya kamata a rika daukarsu da muhimmanci. Kuma kamata ya yi a rika ba su dama kamar sauran manyan kasashe. Wannan tamkar nanata kira da kokarin da kasar Sin ne na ganin duniya ba ta kasance karkashin ikon wata kasa ko wasu tsiraru ba.

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

Hakika kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kai da ci gaban kasashen Afrika.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara
Daga Birnin Sin

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Daga Birnin Sin

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Gasar Wasannin Asiya Ajin Masu Bukata Ta Musaman Ta Hangzhou Ta Bayyana Kulawar Da Sin Take Baiwa Wannan Rukuni Na Al’umma

Gasar Wasannin Asiya Ajin Masu Bukata Ta Musaman Ta Hangzhou Ta Bayyana Kulawar Da Sin Take Baiwa Wannan Rukuni Na Al’umma

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.