Dan wasa Harry Maguire dai yana ci gaba da fuskantar suka daga bangarori da daman a magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da kuma na tawagar kasar Ingila sakamakon rashin kokarinsa.
Sai dai mai koyar da ‘yan wasan kungiyar Manchester United Erik ten Hag ya ce ya yarda da kwallon kyaftin din kungiyar Harry Maguire duk da sukar da ake yi wa dan kwallon saboda rashin tabuka komai.
- Wakilin Sin Ya Yi Cikakken Bayani Kan Sakamakon Da Jihar Xinjiang Ta Samu Wajen Kare Hakkin Bil Adam
- Duba Ga Dokokin Da Samari Ke Kakaba Wa ‘Yan Matan Da Za Su Aura
Maguire na shan suka daga magoya bayan kungiyar tare da magoya bayan kasarsa bayan kuskuren da ya tafka a wasansu da Jamus a wasan da suka yi 3-3 a gasar cin kofin Nations League.
“Ina kare shi saboda na yarda kuma na amince da shi kuma maganar dai a kan shi ce, kuma na yi imani cewa zai iya abin da duk muke bukata, zai dawo kokarinsa kamar yadda yake a baya, ni na yarda da haka” In ji Ten Hag.
Ten Hag ya fi sanya Lisandro Martinez da kuma Raphael barane a matsayin ‘yan bayan sa da yake sanya wa, ya yin da yake bai wa Bruno Fernandez kyaftin a ‘yan makonnin nan kuma wasa uku kacal Maguire ya bugawa Manchester United a wannan kakar.
Ten Hag ya ci gaba da cewa “Duk da cewa baya cikin ‘yan wasa 11 na farko da ake fara wasa da su amma yana atisaye sosai, Ten Hag ke cewa kan dan wasan me shekara 29 wanda ya koma kungiyar daga Leceister City.
A wannan makon takwaransa na Ingila da Manchester United Luke Shaw yace bai taba ganin irin sukar da ake yi wa Maguire ba a tahirin kwallon kafa ba duk da cewa shima a baya ya sha suka.
Maguire bai buga karawar da Manchester United ta yi ba da abokiyar hamayyarta Manchester City a ranar Lahadi saboda raunin da ya ji kuma ana ganin zai dauki wata daya yana jiyyar ciwon da yaji a tawagar Ingilan.