A wani rahoto da BBC Hausa ta fitar ya nuna yadda fina-finai masu dogon zango aka kasa kawo karshensu duk da tsawon lokacin da aka kwashe ana yin su, masu kallon fina-finan Hausa na ci gaba da tambayar wai me ya sa ba a kawo karshen fina-finan Hausa masu dogon zango, tambayar da har yanzu ba ta samu cikakkiyar amsa ba.
Daga cikin fina-finan da aka dade ana yi akwai fim din Izzar so mai dogon zango, wanda ya kasance cikin fina-finai masu dogon zango na farko-farko.
Fim din wanda aka fara sakin fitowa ta daya a ranar 12 ga watan Afrilun shekarar 2020, an yi fitowa (episode) har sau 100, sannan aka koma Izzar so sabon salo daga fitowa ta 101, zuwa fitowa ta 150, daga nan kuma sai su ka koma Izzar so takun farko, wanda shi ake yi yanzu, kuma ana fitowa ta 10.
- Gwamnati Za Ta Goyi Bayan Shirin Fim Kan Tarihin Shekaru 25 Na DimokuraÉ—iyyar Nijeriya
- Shirin Fim Kan Cikar Nijeriya Shekaru 25 A Kan Turbar Dimokuradiyya: Tasiri Da Muhimmanci
Sai dai ba fim din Izzar so ne ya fi dadewa ana yi ba, domin akwai fim din dadin kowa na tashar Arewa24, wanda zuwa yanzu an haura shekara 10 ana yi, fim din Gidan Badamasi wanda shi ma ake kallo a tashar Arewa24, a baya an sanar da kammala shi, amma yanzu an dawo an ci gaba.
Haka akwai finafinai da dama masu dogon zango da wasu suke ganin kamar ya dace a ce an dakatar da su, an shiga wasu, a fina-finan Hausa masu dogon, ana tunanin yanzu fim din Watarana a kano na Abubakar Bashir Maishadda, wanda yake da fitowa biyar kacal ne aka nuna shi a manhajar Arewa on demand na Arewa24 aka gama.
Wannan ya sa murnar da wasu ke yi ta komawa da haska finafinan Hausa masu dogon zango a tashar YouTube ta fara komawa ciki.
Me ya sa ba a gamawa din?
BBC Hausa ta ci gaba da cewa wani faifan bidiyo na wata tattaunawa da jagoran shirin Izzar so, Ahmad Lawan ya yi a tasharsa ta Bakori TV, ya ce masu kallo ne ba su gaji da kallon shirin ba, shi ya sa ba zai daina ba.
Ya ce kasancewar Youtube ya dade kudu, amma bai je arewacin Nijeriya ba ne ya sa su ka gwada domin su koya wa mutanen arewa kallon fim a YouTube, shi kuma wannan fim din ya na ciki, ko in ce shi ne daya tilo da ya koya wa mutane kallo a YouTube, kuma mutane ba su gaji da kallonsa ba,” in ji shi, inda ya kara da cewa, “ka ga babu dalilin da zai sa mu daina.”
Na biyu kuma shi ne akwai abubuwa na addini da muke kawowa da suke tasiri a zukatan al’umma kamar soyayyar Annabi SAW, sannan akwai abubuwa da dama da an manta su a cikin addini, idan muka nuna sai su zama matashiya, fitaccen jarumin ya kara da cewa a sanadiyar dim din akwai akalla mutum uku da suka karvi addinin musulunci, wanda a cewarsa hakan na cikin abubuwan da suka sa bai daina fim din ba.
Hakazalika fitaccen marubuci kuma furodusa, Nazir Adam Salihi, wanda yake cikin marubuta shirin dadin kowa mai dogon zango, kuma forudusan shirin Gidan Badamasi, ya ce nan gaba kadan za a fara kammala wasu shirye-shirye.
Ya ce “mu ne muka fara fina-finan nan masu dogon zango, kuma sama da shekara 10 ne da suke wuce ne muka fara zuwa yanzu, a Turai irin su Ingila kuma akwai finafinai masu dogon zango da aka yi shekara 65 ana yi ba a gama ba, ka ga ba za a yi gaggawar cewa ba a gama na Hausa mu da muka fara sama da shekara 10 da suka wuce.”
Sai dai ya ce akwai wasu fina-finai da aka gama daukarsu, “nan gaba kadan zuwa shekara mai zuwa za a kammala wasu fina-finan, a shiga wasu daban, a game da ko ana karancin labaran ne, marubucin ya ce Hausawa na da labarai masu kyau da inganci.
A karshe Salihi ya ba marubuta shawarar su dage da karatu da bincike da kuma natsuwa wajen rubuta labaransu, da yake jawabi kan lamarin, dokta Muhsin Ibrahim, malami a Jami’ar Cologne da ke Jamus ya ce wannan matsala ce ga masana’antar, wadda ba za ta haifa da mai ido ba.
A cewarsa, abin da yake faruwa shi ne masu shirya fina-finan su na fargabar idan suka daina fim din ba dole ba ne wanda za su fara din ya samu karvuwa kamar shi, sai dai ya ce wannan matsala ce babba saboda “babu labarin da ba shi da karshe kuma duk hakurin mai kallo ana iya kure shi.”
Ya ci gaba da cewa duk masana’antun fim na duniya da suka ci gaba a duk labarin da suka tsara, akwai farkonsa da tsakiya da karshe, shi ya sa nake ganin wannan rashin dabara ce saboda yan kallon da suke tunani dai dole sai sun kubuce musu, musamman idan sun samu wani fim da ya fi wannan.
Muhsin ya kara da cewa ya kamata a ce duk wani fim da za a fara, a san cewa za a iya fara wani wanda ya fi shi ko kuma ya gaza shi, misali shirin Labarina mai dogon zango, duk da cewa Aminu Saira ya rike sunan, ai na biyu ya fi na farko karvuwa, shi fim din kamfanin Uk Entertainment ai Garwashi ya fi Fatake karvuwa,” in ji shi.
Ya ce rashin gama fim yana rage wa masu kallo karsashin ci gaba da kallon saboda fargabar ko sun fara kallo, suna tunanin ba za a gama ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp