Tun daga watan Fabrairun bana, tattaunawar da ake yi a kan Intanet ciki har da shafin sada zumunta na yanar gizo na X mai taken “Adawa da sayen kayayyakin kirar Amurka” na kara samun karbuwa.
Yawan mutanen kasar Denmark miliyan 6 ne kawai, amma yawan mambobin rukunin tattaunawa dake yin kira da a nuna adawa da kayayyaki kirar Amurka da harshen Danish a shafin FACEBOOK ya kai 72,000 a yanzu, inda adadin ya rika karuwa daga 1000 a watan Janairu.
- ECOWAS Ta Kaddamar da Dakarun Yaƙi da Ta’addanci
- Ukraine Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Wata Guda Da Rasha
To, kowa ya san kasashen Turai kawayen Amurka ne da suke dasawa da yaukaka dankon zumunci a tsakaninsu, amma me ya sa a wannan karo jama’ar Turai suke nuna adawa da kayayyaki kirar Amurka?
Dalilin da ya haifar da hakan kai tsaye shi ne ra’ayin da shugaba mai ci na kasar Amurka ke bayyanawa kan batun tsibirin Greenland. A ganin wasu jama’ar Turai, Amurka ta yi shisshigi cikin harkokin gidan sauran kasashe, a wani bangare na daban kuma akwai batun rikicin Ukraine. Baya ga hakan akwai batun harajin kwastam wanda shi ma yana da alaka sosai da zamantakewar rayuwar jama’ar Turai.
Ikon mulkin kasa da tsaro da tattalin arziki, muhimman muradu 3 ne da Turai ke mai da matukar hankali a kansu, wadanda yanzu suna fuskantar barazana da kalubale daga Amurka. A bangaren ’yan siyasar Amurka kuwa, matakin adawa da kayayyakinta da jama’ar Denmark suka dauka na aika mata da kashedi ne cewa, matukar an kara tunzura lamarin, ba wanda zai yi asara mai tsanani illa kamfanonin Amurka. Kuma hatta tsarin dake tsakanin mabambantan bangarori zai yi mummunan lalacewa bayan matakan adawa da mayar da martani da dama da za a rika yi wa juna.
A wani bangare na daban kuwa, dole ne ’yan siyasar Turai su yi tunani cewa, jama’arsu sun dauki irin wannan mataki ne ba ma kawai bisa bukatunsu na sayayya ba, har ma ya kasance mataki ne na nuna adawa da babakeren Amurka, da bukatunsu na dogaro da kansu a bangaren manyan tsare-tsare.
Huldar Amurka da Turai ta wannan fuskar ta yi hannun riga da ainihin ma’anar zumunci, inda lamarin ya yi rauni matuka, kuma tabbas matukar Turai ba ta nemi dogaro da kanta ba, za ta yi asara daga barazana da kalubalen da Amurka take haifarwa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp