A gabar da duniya ke fuskantar matakan kariyar cinikayya daga wasu sassa, da tarin kalubale dake tarnaki ga bunkasar tattalin arzikin duniya, sassan kasa da kasa na kara mayar da hankali ga hadin gwiwa tare da kasar Sin, inda ake kara ganin yadda ake raba ribar nasarar da Sin din ke samu ta fannin ci gaba da sauran kasashen duniya.
Kamar yadda muka gani, a shekarar da ta shude, kasar Sin ta aiwatar da sabbin tsare-tsare masu ma’ana, don kara bude kofofinta na raya tattalin arziki mai inganci, inda kuma ta cimma manyan nasarori wajen habaka hadin gwiwa da sauran sassa, a tafarkin bunkasa ginshikan shawarar nan ta “ziri daya da hanya daya” ko BRI. Sanin kowa ne cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” da Sin ta gabatarwa duniya, ta zamo wani muhimmin dandali na ingiza tafiya tare tsakanin sassan kasa da kasa a fannin samar da hajoji da hidimomi, ta kuma bayar da wata dama mai kyau, ta cin gajiya tare, da dunkule tattalin arzikin duniya wuri guda.
- ECOWAS Ta Kaddamar da Dakarun Yaƙi da Ta’addanci
- Ukraine Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Wata Guda Da Rasha
Wannan shawara da aka gina bisa tushen yin aiki tare, da gina moriya tare, ta samu amincewar sama da kasashen duniya 150, da hukumomin kasa da kasa sama da 30. Yayin da a daya bangaren ake ta kara fadada sassan da shawarar ke kunsa, da daga matakan hadin gwiwa da ake cimmawa a karkashin shawarar.
Shaidun gani da ido sun nuna mana yadda shawarar BRI ta samar da dandali na hadin gwiwa, don samar da ci gaban bai daya, da taimakawa wajen gina ababen more rayuwa a kasashe masu tasowa, da gaggauta tafiyarsu a kan tafarkin zamanantar da kai.
Shawarar BRI ta nuna mata basirar kasar Sin wajen aiwatar da matakai da za su kai ga cike gibin dake akwai na ci gaba tsakanin kasashen duniya. Kazalika, karkashin tsare-tsaren aiwatar da shawarar, da salonta na gudanar da hadin gwiwa a matakai daban daban, BRI na ci gaba da shawo kan manyan kalubalen dake addabar duniya baki daya.
Masharhanta da dama na da imanin dorewar matakai na aiwatar da wannan shawara tsakanin kasashen duniya, zai ci gaba da samar da sabon kuzari, wajen magance batutuwan dake addabar sassan kasa da kasa musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, da koma bayan ci gaban wasu sassa, da raunin jagoranci a wasu bangarori.
La’akari da hakan, ma iya cewa shawarar BRI na samar da wani sabon mafari na bunkasa hada-hadar cinikayya, da raya tattalin arzikin duniya baki daya, yayin da a daya hannun take wanzar da cudanya mai ma’ana, da tafiya kan tafarkin neman ci gaban daukacin bil’adama ba tare da ware wani bangare ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp