Mene ne ma’anar teku ga Japanawa? Kasar Japan na fuskantar teku a bangarori hudu, wato kasar Japan ta kasance kamar wani tsibiri ne a cikin teku. Sakamakon haka, Japanawa sun kirkiro “ranar teku” don bayyana yadda suke ba da muhimmanci kan teku, tare da bayyana fatansu na samun bunkasuwar kasarsu. Tun lokacin Jomon na tarihin yankin, Japanawa na da alaka da teku. A bangarori daban-daban na rayuwarsu, suna da mu’ammala matuka da teku. Mai zana hoto da ya yi suna sosai a duniya Katsushika Hokusai, ya kwashe duk rayukansa yana zana teku, don bayyana yadda Japanawa suke kaunar teku.
Amma, duk da cewa Japanawa na jinjinawa, da girmamawa teku a zukatansu, gwamnatin Japan ta yanke shawarar zubawa teku ruwan dagwalon nukilya. Wannan ruwan da aka sarrafa na cike da sinadarai masu guba iri na nukiliya, kamar su Tritium, da carbon-14, da cobalt 60, da strontium 90 da sauransu, kuma da wuya a kawar da su kwata kwata. To amma abun tambaya shi ne, ko me ya sa gwamnatin Japan ke kokarin keta al’adunta na martaba teku ta hanyar zuba masa wannan ruwa mai hadari?
Ba shakka, moriya ce. Ajiye wannan ruwan zai haifar da kashe kudade da dama, amma zubar da shi a cikin teku na da araha. Dole ne gwamnatin Japan ta dudduba zuciyarta, ta yi watsi da shirin a maimakon yunkurin fitar da matakan ba da kariya ga shirinta, da kuma yin hadin kai da sauran kasashe don kiyaye muhallin teku, ta yadda za su kiyaye al’adunsu. (Mai zana da rubuta: MINA)