A yayin bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin CIIE karo na 7 da ake gudanarwa a birnin Shanghai a gabashin kasar Sin, ana nuna dimbin kayayyakin zamani marasa gurbata muhalli, lamarin da ya nuna yadda ake ta yin kirkire-kirkire a duniya.
A bukukuwan CIIE 6 da aka gudanar a baya, an nuna sabbin kayayyaki, fasahohi, da hidimomi kusan 2500. An mayar da bikin CIIE a matsayin dandalin da akan fara nuna sabbin kayayyaki, fasahar zamani, da hidimomin masu yin kirkire-kirkire a duniya. Me ya sa haka?
- Gwamnan Kano Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin 2025 Na Naira Biliyan 549.1
- Kingibe Ya Yaba Wa Tsare-tsaren Bunkasa Ilimi Ga Matasa Na Buratai
Bikin na CIIE, bikin baje koli ne na farko da gwamnatin kasa ta shirya a duniya dangane da kayayyakin da ake shigowa da su. Ya samar da dandalin baje kolin sabbin kayayyaki masu inganci da suka shiga kasuwar kasar Sin, tare da samar da kyakkyawar hanyar yin cinikin dimbin sabbin kayayyaki da sabbin fasahohi. Haka kuma kasuwar kasar Sin mai yawan mutane fiye da biliyan 1.4 ciki har da masu matsakaicin kudin shiga fiye da miliyan 400, ta samar wa sabbin kayayyaki da sabbin fasahohin kasa da kasa wurin gwaje-gwaje da hanyar shiga kasar Sin. Har ila yau a shekaru fiye da 10 da suka gabata, kasar Sin ta yi amfani da damar juyin juyin hali ta fuskar kimiyya da fasaha da sauye-sauyen masana’antu na sabon zagaye, wajen aiwatar da manyan tsare-tsaren samun ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire, tare da samar wa kamfanonin wajen yanayin yin kirkire-kirkire.
An yi hasashen cewa, a bukukuwan CIIE masu zuwa, kamfanonin waje za su samu kwangiloli, kasuwanni, sabbin ra’ayoyi da ma damammakin da zamanantarwa irin ta kasar Sin take samarwa. (Tasallah Yuan)