A taron dandalin hadin gwiwar kasa da kasa karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin a kwanan baya, Najeriya da kasar Sin sun zurfafa hadin gwiwarsu, inda suka kulla yarjejeniyoyin gudanar da wasu ayyuka, da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 2, wadanda suka shafi zuba jari da wasu kamfanonin Sin za su yi a Najeriya, don gina masana’antun hada motoci masu amfani da wutar lantarki, da na’urorin da suke iya shawagi da ake kira “drone”, gami da batir na motoci, da dai sauransu.
Ban da haka, wasu kamfanonin kasar Sin 10, sun bayyana niyyar zuba jari a Najeriya don raya wasu ayyukan da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 4, wadanda suka shafi kera kayayyaki masu amfani da makamashin hasken rana, da kera motoci, da makamashi mai tsabta, da aikin gina yankin masana’antu, da na’urorin sarrafa iskar gas, da aikin koyar da fasahohin sana’o’i, da na’urorin samar da wutar lantarki masu inganci, da dai makamantansu.
- Kasar Sin Ta Bukaci Tsagaita Wuta Da Samar Da Agajin Jin Kai A Zirin Gaza
- An Yi Bikin Kaddamar Da Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Mutane Masu Bukata Ta Musamman Ta Asiya A Hangzhou
Bisa tantance wadannan ayyuka, za a iya ganin halayensu: Da farko, dukkansu sun shafi fasahohin zamani, da sabbin masana’antu masu kyakkyawar makoma. Na biyu, da yawa daga cikin ayyukan sun shafi yadda za a gina masana’antu da kayayyakin more rayuwa a Najeriya, kuma a tabbatar da mika fasahohi ga Najeriya, ta yadda ayyukan za su taimaki Najeriya wajen raya bangaren masana’antu. Na uku, a cikin ayyukan akwai hadin gwiwar da za a yi a fannonin koyar da ilimin sana’a, da kyautata fasahar samar da wutar lantarki, da raya tattalin arziki tare da kare muhalli, wadanda ke neman biyan bukatun Najeriya ta fuskar inganta zaman rayuwar jama’a. Wadannan halaye sun dace da taken taron Ziri Daya da Hanya Daya na wannan karo, na “aiwatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya cikin inganci”.
Wannan take asalinsa shi ne ra’ayin “samun ci gaba mai inganci” na kasar Sin, wanda ya shafi kokarin kirkiro sabbin fasahohi, da inganta harkoki, da kare muhalli, gami da horar da ma’aikata, don neman samun ci gaba mai inganci, da sabbin fasahohi, da kyawun muhalli, da jin dadin zaman rayuwa, ta yadda za ta tabbatar da ci gaban tattalin arziki, da na al’umma mai dorewa.
Wannan ra’ayi ya riga ya zama wata muhimmiyar manufar kasar Sin a fannonin raya tattalin arziki, da gudanar da sauran ayyuka. Yanzu kasar Sin na neman yin amfani da shi wajen inganta hadin gwiwarta da sauran kasashe, da haifar musu da ci gaba, da zamanantarwa masu inganci.
Sai dai me ya sa kasar Sin ke son raba ilimi da dabaru, da fasahohi masu muhimmanci tare da sauran kasashe? Me ya sa take iya nuna cikakken sahihanci, a kokarinta na taimakawa Najeriya da sauran kasashen dake nahiyar Afirka samun ci gaba? Amsa ga wadannan tambayoyi ta shafi tsarin siyasa na kasar Sin.
Kasar Sin kasa ce mai rungumar tsarin siyasa na Gurguzu, hakan ya tabbatar da cewa, ba za ta yi kama da kasashen yammacin duniya ba, wadanda ke dogaro kan jari, da barin jarinsu ya yi tasiri yadda ya ga dama.
Manyan ‘yan kasuwa masu jari a hannunsu na kasashen yamma, suna son yin babakere a bangarorin fasahohi, da kudi, da tamburan kayayyaki, da shawo kan tsarin samar da kayayyaki, ta yadda za su samu karfin kare wani tsarin dake amfaninsu a duniya, don tabbatar da samun mafi yawan moriya. Wannan shi ne dalilin da ya sa kasashe masu tasowa gamuwa da wahalhalu yayin da suke neman raya tattalin arziki, a karkashin wani tsarin tattalin arziki na kasa da kasa da su kasashen yamma ke jagoranta.
A nata bangare, gwamnatin kasar Sin tana taka tsan-tsan game da illar da jari zai iya haddasawa ta rashin daidaito tsakanin al’ummu da kasashe, kana kasar ta yi kokarin kawar da gibin da ake samu tsakaninsu, don tabbatar da ci gaban tattalin arziki, da na al’umma mai dorewa a duniyarmu.
Saboda haka, kasar Sin tana kokarin kawar da talauci, da kyautata zaman rayuwar jama’a a cikin gida, gami da neman samun daidaituwa, da hadin kai, da ci gaba tare a duniya, da gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya. Wannan shi ne dalilin da ya sa kasar Sin ke son ganin sauran kasashe, ciki har da Najeriya, sun samu ci gaba mai inganci. (Bello Wang)