Ana ta kara samun kasashen Afirka da suke korar sojojin kasashen yamma a ‘yan kwanakin nan. A jawaban taya murnar shiga sabuwar shekara ta 2025 da shugabannin kasashen Cote d’Ivoire da Senegal suka gabatar a kwanan nan, baki dayan shugabannin biyu sun bukaci kasar Faransa da ta janye sojojinta daga kasashensu, wato daga shekarar nan ta 2025. Idan ba mu manta ba, tuni kasashen Faransa da Amurka da Jamus suka janye sojojinsu daga kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijer, bisa bukatar gwamnatocin rikon kwarya na kasashen. Kasar Chadi ma a watan Disamban bara ta bukaci Faransa da ta janye sojojinta daga kasar kafin ranar 31 ga watan Janairun bana.
To, amma me ya sa kasashen Afirka suke ta korar sojojin kasashen yamma?
Muna iya gano amsar tambayar daga zancen shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye a yayin da yake tattaunawa tare da manema labarai a watan Nuwamban da ya gabata, inda ya ce, kasar Senegal ta cika shekaru 64 da samun ‘yancin kanta, don haka ita kasa ce mai mulkin kai, kuma kasar da ke da ‘yancin mulkin kanta ba za ta iya hakuri da kasancewar sansanin soji na Faransa a cikinta ba.
A shekarar 2011, bisa jagorancin kasashen Amurka da Faransa, kungiyar tsaro ta NATO ta dauki matakan soja na tsawon watanni 7 a kasar Libya domin hambarar da tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi, matakin da daga bisani ya haifar da tashe-tashen hankula a yankunan da ke makwabtaka da Libya, kuma a sabili da haka, aka samu yawaitar sumogar ta makamai da ma kafuwar kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Daga baya, a shekarar 2013, Amurka da Faransa da ma sauran kasashen yamma suka fara tura sojojinsu zuwa Nijer da Burkina Faso da Chadi da Mali da sauran wasu kasashen da ke yankin Sahel, da sunan yakar kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi. Sai dai, hakan bai haifar da da mai ido ba, ganin yadda kasashen suka yi ta fama da karuwar talauci da rikice-rikice. Abin da ya sa karin al’ummar kasashen Afirka suka gane cewa, don yin katsalandan cikin harkokin gidansu, da kwace albarkatunsu ne, kasashen yamma suke girke sojojinsu, dalilin haka suka fara yi musu tutsu da nuna kin jinin sojojin.
“Ko a yankunan da aka girke sojojin Faransa, ’yan ta’adda na ci gaba da kai hare-hare ga fararen hula. Ke nan, mece ce ma’anar kasancewarsu idan sun kasa kiyaye tsaro?” in ji Michael Ndimancho, wani shehun malami na kasar Kamaru.
Haka nan, wani marubucin kasar Nijer, Abdoulaye Sissoko ya yi nuni da cewa, burin da Amurka ke neman cimmawa shi ne tabbatar da ikonta a yankin kawai a maimakon yakar kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Ban da haka, kasashen yamma sun taba yin mulkin mallaka ga akasarin kasashen Afirka, wadanda ko bayan da suka samu ‘yancin kansu, kasashen na yamma sun ci gaba da nuna babakere da neman tabbatar da ikonsu a kasashen. Wata mukalar da cibiyar nazarin tsare-tsare da harkokin kasa da kasa ta Amurka (CSIS) ta fitar ta yi nuni da cewa, kasashen Turai da Amurka kan dauki wasu matakai na tilasta wa kasashen Afirka bin turbar da suke so, matakin da a hakika yana nuna ci gaba da mulkin mullakarsu ne, wanda kuma tabbas yana haifar da talauci da koma baya ga kasashen Afirka da dama.
Tabbas, kasashen Afirka na farkawa. Kuma yadda kasashen ke korar sojojin kasashen yamma ya nuna aniyarsu ta neman ‘yancin kansu na hakika da kyamar sabon salon mulkin mallaka na kasashen yamma, kana abin da suke so shi ne tabbatar da zamantakewa ta daidai-wa-daida da hadin gwiwar cin moriyar juna da sauran kasashe.
Don haka, ya kamata kasashen yamma su gane cewa, lokacin yi wa kasashen Afirka duk abin da suka ga dama tuni ya wuce. Dole ne a bi ka’idar martaba juna, da zaman daidaito, da cin moriyar juna wajen aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka, sabo da ta haka ne za a kai ga tabbatar da ci gaba, da tsaro na bai daya.(Lubabatu Lei)