Shigarmu sabuwar shekara ta 2025 ke da wuya, ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya fara ziyara a nahiyar Afirka. A jiya ya isa kasar Namibia, daga baya zai kuma ziyarci kasashen Congo Brazaville, da Chadi, gami da tarayyar Najeriya. Hakika yadda ministan waje na kasar Sin kan yi ziyararsa ta farko a duk sabuwar shekara a nahiyar Afirka, ya riga ya zama al’adar kasar Sin ta fannin diplomasiyya, wadda ba a taba dakatarwa ba tsawon shekaru 35 da suka wuce.
Sai dai mene ne dalilin da ya sa aka dauki wannan manufa? Wang Yi, ministan wajen kasar Sin ya ba da amsa jiya, yayin da yake ganawa da shugabar kasar Namibia mai jiran gado, Netumbo Ndaitwah. A bayaninsa, kasar Sin ta dauki matakin ne saboda yadda take ba zumunci mai karfi a tsakanin bangarorin Sin da Afirka muhimmanci. Ban da haka, kasar na son nuna wa duniya cewa, duk wani yanayin da ake ciki, ita aminiyar kasashen Afirka ce, da za su iya dogaro a kanta, kuma za ta goyi bayansu a dandalin siyasar kasa da kasa a ko da yaushe.
- An Rantsar Da Sabon Shugaban Ƙasar Ghana, John Mahama
- Gwamnatin Sakkwato Ta Yi Alƙawarin Tallafa Wa Waɗanda Gobara Ta Shafa A Kasuwar Kara
Bugu da kari, za a ga yadda maganar jami’in na Sin ta samu shaida daga zancen tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo. Yayin da yake hira da manema labaru a garin Abeokuta a kwanan nan, Mista Obasanjo ya ce kasar Sin ”babbar aminiyar hadin gwiwa ce”. A cewarsa, huldar dake tsakanin Afirka da Sin tana amfanar da junansu, kana kasar Sin tana kyakkyawar rawa wajen kiyaye adalci. Sa’an nan, an kulla huldar hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Sin ne bisa tushen girmama juna, da rabon daidai-wa-daida, saboda haka huldar na da makoma mai haske.
To, bayan karanta kalaman Mista Wang Yi, da na Mista Obasanjo, watakila kai mai karatu za ka so ka yi tambayar cewar, mene ne tushen zumunci da huldar hadin gwiwa tsakanin Afirka da Sin? To, a ganina, asalin tushe mai muhimmanci kan lamarin shi ne akidar diflomasiyya ta kasar Sin, wato gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai-daya. Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ne ya gabatar da wannan akida, wadda ta jaddada muhimmancin huldar dogaro da juna tsakanin kasashe daban daban, da kare moriyarsu ta bai-daya, da samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa, gami da kulawa da al’amuran duniya cikin adalci. Kana akidar ta bukaci a lura da moriya da damuwar sauran kasashe, da kokarin tabbatar da ci gaban mabambantan kasashe na bai-daya.
Asalin akidar gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya shi ne tunanin gargajiya na Sinawa, kamar su ”neman tabbatar da jituwa a duniya” da ”darajanta zaman lafiya”, gami da ”mai da adalci a gaban moriyar kashin kai”. Ban da haka, akidar ta dace da babbar manufar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, mai mulki a kasar, ta kuma yi kokarin tabbatar da jin dadin jama’a, da ci gaban harkokin dan Adam. Kana ita ce sabuwar dabarar da kasar Sin ta kirkiro don daidaita matsalolin da duniya ke fuskanta.
Tsohuwar dabarar da kasashen yamma kan yi amfani da ita wajen wanzar da tsarin duniya, ita ce sanya kowa ya shiga takara da juna bisa bukatar kare moriyar kai, har zuwa lokacin da aka samu wani yanayi na daidaituwa. Sai dai tsohuwar dabarar ta kasa biyan bukatun dan Adam na tinkarar dimbin kalubaloli a wannan zamanin da muke ciki, abin da ya sa ake samun yawaitar tashe-tashen hankula a wurare daban daban. Saboda haka ana bukatar wata sabuwar dabara. Wannan bukata ta sa aka samu akidar gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai-daya.
Kasar Sin da kasashen Afirka suna aiwatar da akidar daga fannoni 2. Na farko, shi ne hadin gwiwarsu ya nuna yadda suke kokarin kare moriyar bai-daya, da neman samun ci gaba tare. Kana na biyu shi ne, hadin gwiwar Sin da Afirka na taka muhimmiyar rawa a fannonin kare hakkin kasashe masu tasowa, da adalci da daidaituwa a duniya, gami da wanzar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban.
A cewar Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin, wannan hulda a tsakanin Sin da Afirka ”ta dace da yanayi na adalci, da biyan bukatar dake akwai a zamanin da muke ciki, gami da taimakawa cika burin da al’ummar Sin da Afirka biliyan 2 da miliyan 800 suka sanya a gaba tare. ” (Bello Wang)