“Shawarar tsarin shugabancin duniya” ta zama kalmar da aka sha karanta a rahotannin kafofin watsa labaru na duniya cikin kwanakin baya. Shugabannin wasu kasashe da dama suna ganin cewa, wannan shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin taron koli na SCO da aka gudanar a kwanan baya a birnin Tianjin, tana da muhimmiyar ma’ana a fannin warware matsalolin da suka shafi tsarin shugabancin duniya a yanzu.
A halin yanzu, sauyin karfi a tsakanin kasashe masu ci gaba da ma kasashe masu tasowa shi ne sauyi mafi girma da aka samu a sabon zamanin da muke ciki a fagen kasa da kasa, inda tarin kasashe masu tasowa suka bunkasa da sauri. To sai dai kuma tsarin duniya da ake bi a yanzu haka, bai nuna wani sauyi mai zurfi ba, kuma hakan ya haddasa rashin wakilci, da karfin fada-a-ji na kasashe masu tasowa.
Shawarar tsarin shugabancin duniya ta kunshi muhimman ra’ayoyi, irin su “zaman daidaito wajen mulkin kai”, da “kiyaye tsarin dokoki na kasashen duniya” da “aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori da dama” da dai sauransu, wadanda ke nufin kara fito da muryoyin kasashe masu tasowa a duniya. Saboda haka ne ma kasashe masu tasowa, suka fi mayar da martani kan shawarar. Kafafen yada labaran kasar Iran sun gabatar da sharhi dake cewa, “Al’ummun kasashe masu tasowa ba za su kasance ‘yan kallo kadai ba, maimakon haka za su himmatu wajen shiga ayyukan tsara makomarsu ta gaba.”
A cikin shekaru hudu da suka gabata, kasar Sin ta gabatar da shawarwari guda hudu na kasa da kasa da suka shafi ci gaba, da tsaro, da wayewar kai da ma shugabanci, wadanda suka ba da tabbaci ga duniyarmu da ke fama da tashin hankali. A nan gaba, duk wani canji da yanayin siyasar duniya zai samu, kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye tsarin cudanyar kasashen duniya dake mayar da MDD a matsayin ginshikinsa, da dokokin kasa da kasa a matsayin tushensa. Za kuma ta yi aiki tare da bangarori daban daban, don ciyar da tsarin shugabancin duniya gaba yadda ya kamata, da inganta gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil’adama, da kuma kokartawa wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaban bil’adama. (Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp