A yau Alhamis 13 ga wata, kamfanonin kirar motoci na Turai irin su Volkswagen na Jamus, sun mayar da martani ga aniyar kungiyar tarayyar Turai EU, ta kakaba karin harajin wucin gadi na kaso 38.1 bisa dari, kan motoci masu amfani da lantarki kirar kasar Sin da ake shigarwa Turai. Kamfanonin sun ce abun da ya dace Turai ta yi shi ne yayata manufar sauya alkiblar kamfanonin kirar motocin ta zuwa masu aiki da lantarki, da kare yanayi daga gurbata, maimakon kariyar cinikayya. Wannan ya isa nunawa duniya cewa, burin na EU bai samo asali daga kamfanonin kasashe mambobin kungiyar ba, kuma ba shi da wani amfani illa cimma wasu burika na siyasa.
Karkashin wannan batu, akwai wasu sassa masu burin cimma moriyar kashin kai dake da sarkakiya a cikin kasashen Turai, da kuma wasu mabanbantan mahanga 3 tsakanin kasashen na Turai. Daya daga cikin su ita ce tunanin dakile ci gaban kasar Sin. Sai na biyu, masu tsoron yin kyakkyawar takara tare da Sin. Na uku kuma, tunanin bin ra’ayin Amurka sau da kafa.
To sai dai kuma, bisa abubuwan da aka gani a tarihi, karin haraji ba ya haifar da nasarar takara, kuma ba wanda ke iya cin wata riba daga yakin cinikayya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)