• English
  • Business News
Sunday, September 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Shugabannin Kasa Da Kasa Da Manyan ‘Yan Kasuwa Suka Yi Ta Kawo Ziyara Kasar Sin?

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Me Ya Sa Shugabannin Kasa Da Kasa Da Manyan ‘Yan Kasuwa Suka Yi Ta Kawo Ziyara Kasar Sin?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Daga ranar 18 zuwa 21 ga wata, shugaban kasar Gabon Ali Bango Ondimba ya kawo ziyarar aiki kasar Sin bisa gayyatar da aka yi masa, inda shugabannin kasashen biyu suka tsai da kudurin daga matsayin cikakkiyar dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, zuwa cikakkiyar dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare.

Shugaba Ali Bango ya kasance shugaba na farko daga nahiyar Afirka da kasar Sin ta karba a wannan shekara, haka kuma, yana daga cikin shugabannin kasashe da shiyyoyi da suka kawo ziyara kasar Sin cikin lokacin da bai kai wata daya ba, wato biyowa bayan ziyarar firaministocin Spaniya, da Malaysia da Singapore, da shugaban kasar Faransa, da shugabar tarayyar Turai, sai kuma shugaban kasar Brazil.

  • An Bude Bikin Fina-finai Na Kasa Da Kasa Na Beijing Karo Na 13

Ban da su kuma, kusan manyan jagororin kamfanonin kasa da kasa guda 100 da suka hada da Apple, da Mercedes-Benz, da makamantansu ma suka ziyarci kasar Sin, don neman damammaki na kasuwanci.

Amma me ya sa shugabannin kasa da kasa da manyan ‘yan kasuwa suka yi ta kawo ziyara kasar Sin? A yanayin da ake ciki na rashin samun kwanciyar hankali da kuma rashin tabbas, me ya sa kasashen duniya suka rika zura ido ga kasar Sin?
Domin amsa tambayoyin, za mu fara da yin nazari kan yanayin siyasar da ake ciki a duniya, inda yanzu haka ake fuskantar tashin hankali da sauye-sauye, inda kasashen yamma da ke karkashin jagorancin Amurka suka yi ta haifar da rarrabuwar kawuna, da yin fito-na-fito a tsakanin kasashen duniya, matakin da ya jawo damuwa da rashin jin dadi ga kasashe da dama. Kasar Sin a nata bangaren, tana ganin duniya ta ishi dukkanin kasashe su bunkasa kan su, kuma ta ba da shawarar kafa sabon salon dangantakar kasa da kasa mai girmama juna, da adalci, da hadin gwiwar cin moriyar juna, inda bi da bi, ta gabatar da manufar gina zaman al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, da shawarar ziri daya da hanya daya, da shawarar raya duniya, da shawarar kiyaye tsaron duniya, da kuma shawarar wayin kai ta duniya, wadanda suke kunshe da tunanin gargajiya na kasar na rungumar zaman lafiya da kiyaye bambancin juna, wadanda kuma suka samu karbuwa daga akasarin kasashen duniya.

Shugaban kasar Gabon kafin ya fara wannan ziyara ma ya yaba da wadannan shawarwari da kasar Sin ya gabatar, yana mai cewa, shawarwarin za su taimaka ga kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya, tare da tabbatar da ci gaban kasa da kasa. Shi ma shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a yayin ziyarar sa ya ce, Faransa na nacewa ga manufar diflomasiyya mai ‘yanci, kuma tana ganin ya kamata Turai ta kiyaye ‘yancinta ta fannin tsare-tsarenta, har wa yau ya bayyana rashin amincewa da jawo rarrabuwar kawuna, da yin fito-na-fito a tsakanin kasa da kasa.

Labarai Masu Nasaba

Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu

A fannin tattalin arzikinta kuma, tun bayan da kasar Sin ta inganta matakan kandagarkin annobar Covid-19, tattalin arzikin kasar Sin ya farfado. Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta samar da kwanan nan sun shaida cewa, a farkon watannin ukun bana, mizanin tattalin arziki na GDP na kasar ya kai yuan trilliyan 28499.7, wanda ya karu da kaso 4.5% bisa na makamancin lokacin bara, har ma hukumomin kasa da kasa da dama sun kyautata hasashensu kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar cikin wannan shekara.

Kasancewarta kasa mafin karfin tattalin arziki na biyu a duniya, farfadowar tattalin arzikin kasar na amfanar duniya baki daya a maimakon ita kanta. Babbar darektar asusun ba da lamuni na duniya IMF, Kristalina Georgieva ta ce, farfadowar tattalin arzikin kasar Sin na nufin kasar Sin ka iya bayar da gudummawar da za ta kai kaso 1/3, ko ma fiye da haka ga ci gaban tattalin arzikin duniya a bana. Abu mafi muhimmanci kuma shi ne yadda kasar Sin ke nacewa ga kiyaye dunkulewar ci gaban duniya, da ma inganta bude kofarta ga ketare, ta yadda karin kasashen duniya za su ci gajiyar bunkasuwarta.

Daidai da yadda Ola Källenius, shugaban darektocin kamfanin Mercedes-Benz, wanda ya kawo ziyara kasar Sin kwanan baya ya fada, cewa “za mu ci gaba da zuba jari ga kasar Sin, kasancewar yadda kasar Sin na kiyaye bunkasuwarta, da bude kofarta ga ketare, ya samar da damammaki masu daraja gare mu.”

Har kullum kasar Sin na rungumar dunkulewar duniya baki daya, kuma tana fatan ganin bunkasuwar kasa da kasa ta bai daya. Ko a tabbatar da ‘yancin kai ta fannin siyasa, ko kuma a dogara ga wasu, ko a bude wa juna kofa ta fannin tattalin arziki, ko kuma a rika yin gaba da juna, duk kasa mai hankali za ta yi zabin da ya dace.(Lubabatu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Shawarar Kasar Sin Game Da Tsaron Kasa Da Kasa Ta Ingiza Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya, In Ji Masana

Next Post

Baba Buhari: Madugun Cin Bashi A Jamhuriya Ta Hudu

Related

Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya
Daga Birnin Sin

Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

11 hours ago
An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu

13 hours ago
Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok

14 hours ago
Aleksandar Vucic: Serbia Na Goyon Bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya Da Kasar Sin Ta Gabatar
Daga Birnin Sin

Aleksandar Vucic: Serbia Na Goyon Bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya Da Kasar Sin Ta Gabatar

15 hours ago
Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya
Daga Birnin Sin

Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya

1 day ago
Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya
Daga Birnin Sin

Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya

1 day ago
Next Post
Baba Buhari: Madugun Cin Bashi A Jamhuriya Ta Hudu

Baba Buhari: Madugun Cin Bashi A Jamhuriya Ta Hudu

LABARAI MASU NASABA

An Cafke Bature Ɗan Shekara 37 Kan Mutuwar Ɗan Nijeriya Mazaunin Birtaniya

An Cafke Bature Ɗan Shekara 37 Kan Mutuwar Ɗan Nijeriya Mazaunin Birtaniya

September 14, 2025
Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina

Rushewar Masa’antu Ya Jefa Al’umma Da Dama Cikin Ƙangin Talauci A Arewacin Nijeriya

September 14, 2025
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

DAPPMAN Ta Soki Matatar Dangote Kan Rage Farashin Man Fetur

September 13, 2025
Yadda Wani Ya Kashe Ƙaninsa, Ya Ɓoye Gawar A Duro

Yadda Wani Ya Kashe Ƙaninsa, Ya Ɓoye Gawar A Duro

September 13, 2025
Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

September 13, 2025
An Kaddamar Da Tashar Watsa Labarai Ta CMG A Chengdu

An Kaddamar Da Tashar Watsa Labarai Ta CMG A Chengdu

September 13, 2025
An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu

An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu

September 13, 2025
An Tsinci Gawar Ɗalibar Jami’ar Taraba A Ɗakin Saurayinta

An Tsinci Gawar Ɗalibar Jami’ar Taraba A Ɗakin Saurayinta

September 13, 2025
Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok

Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok

September 13, 2025
Aleksandar Vucic: Serbia Na Goyon Bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya Da Kasar Sin Ta Gabatar

Aleksandar Vucic: Serbia Na Goyon Bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya Da Kasar Sin Ta Gabatar

September 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.