A watan Maris na shekarar 2013, wato shekaru 10 kacal da suka wuce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da manufar Sin ta hadin gwiwa tare da kasashen Afrika, ta “Nuna gaskiya, da samar da hakikanin sakamako, da kaunar juna, da kuma sahihanci”, yayin da yake ziyara a kasar Tanzania. Wannan alkawari bai tsaya kan magana kawai ba.
Hakika cikin shekaru 10 ko fiye da suka wuce, mun shaida dimbin sakamakon da aka cimma bisa hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afrika: A kasar Najeriya, kasar Sin ta ba da tallafin gina cibiyar nuna ingantattun fasahohin aikin gona, da babban ginin hedkwatar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), wanda ake kokarin gina shi yanzu. Sa’an nan a kasar Habasha, kasar Sin ta gina ginin hedkwatar cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Afrika (Africa CDC) a kyauta. Kana a kasar Masar, kasar Sin ta bude wani shagon Luban cikin jami’ar Ain Shams, don taimakawa raya bangaren koyar da ilimin sana’o’i ga matasan kasar Masar, da dai makamantansu.
A bangaren aikin jinya, ya zuwa karshen shekarar 2021, likitocin da kasar Sin ta tura wa wasu kasashen Afrika sun samar da jinya ga majiyyata ’yan Afrika miliyan 230. Sa’an nan a fannin sufuri, tsakanin shekarar 2000 da ta 2021, kamfanonin kasar Sin sun yi kwaskwarima kan tsohon layin dogo, ko kuma gina sabon layin a kasashen Afirka, da tsayinsu ya wuce kilomita dubu 10, tare da gina wa kasashen Afrika sabbin hanyoyin mota da tsayinsu ya kai kimanin kilomita dubu 100.
Wadannan sakamako sun nuna cewa, taimakon da kasar Sin ke baiwa kasashen Afrika na tare da buri daya, wato taimakawa kasashen Afrika samun ci gaba, da kyautata zaman rayuwar jama’arsu, kamar yadda kasar ke yi a cikin gidanta.
Nagartacciyar huldar hadin kai ta kan haifar da kauna. Bisa aikin da nake a matsayin dan jarida, na taba gamuwa da kwararre a fannin aikin gona dan kasar Sin, wanda ya kwashe shekaru fiye da goma yana kokarin yayata fasahohin aikin gona na zamani a kasar Najeriya; da babban dan kasuwa na kasar Sin, wanda ya jagoranci dansa da jikansa wajen kokarin zuba jari da raya masana’antu a kasashen Afrika; da fitaccen dan siyasa na wata kasar Afrika, wanda ya kan fito fili don kare kasar Sin duk lokacin da ake neman shafa wa kasar bakin fenti, gami da dalibi dan wata kasar Afrika, wanda ya yi aikin sa kai a wata unguwar kasar Sin, a lokacin da yanayin annobar COVID-19 ya fi kamari. Cikin zukatan wadannan mutane, suna kallon al’ummun Sin da na Afirka a matsayin ’yan uwa.
Sai dai, mene ne dalilin da ya sa kasar Sin da kasashen Afrika, kana Sinawa da ’yan Afrika, zama ’yan uwa?
Da farko dai, akwai tushe na sada zumuntar gaske tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, wato huldar daidai wa daida, da ta girmama juna. Dukkan kasar Sin da kasashen Afrika sun taba kasancewa cikin yanayin kunci, inda aka yi musu mulkin mallaka, da cin zarafinsu yadda aka ga dama. Daga baya sun fid da kansu daga mawuyacin hali, inda kasar Sin ta taba ba da taimako ga kasashen Afrika, yayin da suke neman ’yancin kai daga mallakar Turawa ’yan mulkin mallaka, kana kasashen Afrika su ma sun taba tallafawa kasar Sin a kokarinta na komawa cikin Majalissar Dinkin Duniya. Wannan tarihi na cude-ni-in-cude-ka, da raba fara daya, ya sa ba za a taba samun ra’ayi na raini tsakanin Sin da Afrika ba.
Na biyu, kasar Sin da kasashen Afrika suna da buri daya, wato raya kasa, da tabbatar da adalci a fannin huldar kasa da kasa.
Ayyukan da kasashen yamma suka dade, kuma suka fi dora muhimmanci a kai, su ne kokarin mallakar fasahohi, da jari, da kasuwanni, da sauran albarkatu daban daban, don kare fifikonsu, ta yadda za su iya ci gaba da kasancewa a kan wani matsayi na koli, inda suke wa sauran kasashe danniya yadda suka ga dama. Sai dai wannan yanayi ba zai dade ba, ganin yadda kasashe masu tasowa ke kara zama masu fada-a-ji. Ta hanyar raya tattalin arzikinta cikin matukar sauri, kasar Sin ta nuna wa duniya cewa duk wata kasa na da damar tasowa bisa kokarin raya kai. Sauran abun da muke neman gani shi ne yadda kasashen Afrika da kasar Sin za su samu ci gaba na bai daya, bisa kokarin gudanar da hadin kai tsakaninsu.
Abu na karshe shi ne, Sinawa da ’yan Afrika suna da tunani iri daya, wato sun fi yarda da ra’ayi na hadin kai, da more gajiya tare, maimakon ra’ayi na takara da juna don kwatar moriyar kai.
Bisa al’adunsu na gargajiya, Sinawa suna darajanta zaman jituwa, inda suke neman tabbatar da hadin kai, da kwanciyar hankali, da tsari da oda, cikin wani iyali, da kuma al’umma. Wannan al’ada ta zama daya da ta ’yan Afrika, wadanda a kasashensu, a kan ga yadda mambobin wani babban iyali suke zama tsintsiya madaurinki daya, a kokarinsu na kula da tsoffi, da kananan yara, da taimakawa juna, sabanin yadda kasashen yamma ke “daukaka moriyar kai” (wanda ya kan zama “son kai”) da “yin takara” (wanda ya kan zama tamkar abun da ake kira “kashin dankali”). Wannan ma dalili ne da ya sa ra’ayin “Al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya” da kasar Sin ta gabatar ke samun cikakken goyon baya daga kasashen Afrika.
Yawan al’ummar kasar Sin da na kasashen Afrika gaba daya ya kai biliyan 2 da miliyan 700, wanda ya kai fiye da kashi 1 cikin kashi 3 na daukacin mutanen duniya. Saboda haka, Sin da Afrika na kokarin hadin gwiwa da juna, ta yadda zaman lafiya, da hadin kai, da neman ci gaba, da daidaituwa, da adalci za su ci gaba da kasance manyan darajojin da aka fi dora wa muhimmanci a duniya. (Bello Wang)