• English
  • Business News
Tuesday, November 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Syria Ta Bari Ana Amfani Da Sararin Samaniyarta Wajen Kai Wa Iran Hari?

by Rabi'u Ali Indabawa
5 months ago
Syria

Kafofin yada labarai na Syria da ma wasu na yankin Gabas ta Tsakiya sun koka kan yadda sabuwar gwamnatin Syria ta yi gum da bakinta tun bayan barkewar yaki tsakanin Isra’ila da Iran.

Haka nan wasu na mamakin yadda jiragen saman Isra’ila ke ratsawa ta sararin samaniyar Syriya domin kai hare-hare a cikin Iran.

  • Wang Yi: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Rika Tuntubar Juna Domin Kaucewa Rashin Fahimta
  • Za A Kara Amfani Da Rokar Long March-2F Wajen Harba ‘Yan Sama Jannati Zuwa Tashar Sararin Samaniyar Sin

Amfani da sararin samaniyar Syria da jiragen Isra’ila ke yi da kuma amfani da sararin na Syria da Iran ke yi tana harba makamai zuwa Isra’ila ya haifar da asarar rayuka daga dukkanin bangarorin biyu, kuma duk da haka gwamnatin ta Syria ba ta ce uffan ba.

Jaridu da dama a yankin sun yi sharhi kan lamarin, yayin da wasu masana ke cewa rashin tsoma bakin Syriya na nufin mataki ne na tsayawa a tsakiya, wasu kuma na ganin kasar na kallon dukkanin kasashen biyu ne a matsayin makiyanta.

Wani babban jami’in gwamnatin Syriya ya yi watsi da zargin cewa Syriyar na barin Isra’ila na amfani da sararin samaniyarta wajen samun bayani kan makaman da Iran ke harbawa.

LABARAI MASU NASABA

Trump Ya Yi Barazanar Maka BBC A Kotu Tare Da Neman Diyyar $1bn

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

Har yanzu dai gwamnatin Syriya ba ta komai ba game da barna da hasarar rayuka da makamai da kuma jiragen da ake amfani da su da ta sararin samaniyarta ke haifarwa ba.

Shafin Intanet na kafar Enab na kasar Syria ya wallafa wani labari a ranar 15 ga watan Yuni game da shirun da gwamnatin Syriya ta yi kan karakainar da jiragen yaki da makamai masu linzami ke yi a sararin samaniyar kasar.

Wani mai sharhi ya fada wa Enab cewa gwamnatin Syriya ta yanke shawarar tsayawa tsakiya kan lamarin ne kasancewar tana daukar Isra’ila da Iran a matsayin abokan gabarta.

Ya ce: “Babu daya daga cikinsu da za ka bayyana shi a matsayin abokin al’ummar Syriya, kuma dukkaninsu sun taka rawa wajen lalata kasar Syriya.”

Iran na daga cikin manyan kasashen da suka taimaka wa tsohon shugaban Syriya Bashar al-Assad, ita kuma Isra’ila ta kaddamar da daruruwan hare-hare ta sama kan Syriya, kuma ta jibge sojojinta a yankunan tudun mun tsira tun cikin watan Disamba bayan tuntsurar da gwamnatin Assad.

Ya ce gwamnatin Syria a yanzu ta shagalta ne da kokarin daidaita lamurra a cikin gida da kuma karfafa dakon dangantakarta da Turkiyya da kuma kasashen yankin Gulf.

Jaridar da ke kare muradun yankin Larabawa ta ‘Middle East Eye’ ta ruwaito cewa shugaban Turkiyya Receb Tayyib Erdogan ne ya shawarci sabon shugaban Syria Ahmed al-Sharaa cewa kada ya tsoma kansa cikin rikicin.

Saba ka’idar sararin samaniya

Kafar yada labarai ta Syria ta buga rahotanni da dama tana cewa Isra’ila da Iran na karya ka’idojin amfani da sararin samaniyarta, inda ta ce jirage marasa matuka da kuma makamai masu linzami da dama sun fada cikin kasar.

Kafar yada labarai ta Syria – SANA – ta ruwaito cewa wani jirgi mara matuki ya fada kan wani gida a birnin Tartus, kuma daga baya an tabbatar da cewa matar ta rasu sanadiyyar raunukan da ta samu.

Haka nan kafar yada labaran ta SANA ta ruwaito cewa wasu jirage marasa matuka sun fada kan gidajen al’umma a birnin Daraa kuma wani makamai mai linzami ya fada gefen Damascus, babban birnin kasar, inda makamin ya bar wani katon rami.

Sai dai shirun da gwamnatin Syria ta yi kan wannan lamari ya ja hankalin kafafen yada labarai a cikin kasar da kuma kasashen Larabawa.

Yawancin jaridun sun ja hankalin al’ummar kasar cewa kada su kusanci wauraren da makaman ke fadawa.

Sai dai wata majiya ta gwamnati ta karyata ikirarin jaridar Al-Watan, wadda ta ce Ahmed al-Sharaa ya amince wa Isra’ila ta yi amfani da sararin samaniyar Syria wajen samun bayanai kan tafiyar makaman da Iran ke harbawa.

Gidan talabijin na Syria TD da ke da mazauni a Turkiyya ya tattauna da wani mai sharhi, wanda ya ce ya kamata Syria ta kai korafin wajen Majalisar Dinkin Duniya, sannan kuma ta yi amfani da kasashe kawayenta wajen hana karya ka’idojin amfani da sararin samaniyarta.

 

Gidan talabijin dain ya ce yakin na Iran da Isra’ila ya yi cikas ga zirga-zirgar jirage zuwa kasar da kuma datse kai tallafi ga al’ummar kasar masu bukata.

 

Wata jarida ta yankin Larabawa, Al-Kuds Al-Arabi ta ce akwia damuwa kan cewa yakin zai kara raunana tattalin arzikin Syria wanda ba ya da karfi, inda ta ce darajar kudin kasar ta Syria ya fadi da kashi 10 cikin dari tun bayan fara yakin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa
Kasashen Ketare

Trump Ya Yi Barazanar Maka BBC A Kotu Tare Da Neman Diyyar $1bn

November 11, 2025
An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga
Kasashen Ketare

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025
Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto
Kasashen Ketare

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Next Post
Za a Binne Ɗantata A Madina, Za Ai Yi Sallar Ga’ibi A Kano

Za a Binne Ɗantata A Madina, Za Ai Yi Sallar Ga'ibi A Kano

LABARAI MASU NASABA

Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump Ya Yi Barazanar Maka BBC A Kotu Tare Da Neman Diyyar $1bn

November 11, 2025
Rashin Aiki Ga Matasa Babbar Barazana Ce Ga Nijeriya – Obasanjo 

Obasanjo Ya Buƙaci Matasa Su Karɓi Ragamar Shugabanci A Ƙasashen Afrika

November 11, 2025
Yadda Muka Zama Bayin ‘Yan Bindiga -Mazaunin Wani Kauye

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 A Ƙauyen Katsina

November 11, 2025
An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin 

An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin 

November 10, 2025
Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin

Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin

November 10, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano

Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano

November 10, 2025
Sin Ta Dakatar Da Jiragen Ruwan Amurka Daga Biyan Kudi Na Musammam A Tashoshinta Na Ruwa

Sin Ta Dakatar Da Jiragen Ruwan Amurka Daga Biyan Kudi Na Musammam A Tashoshinta Na Ruwa

November 10, 2025
Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa

Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa

November 10, 2025
Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo

Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo

November 10, 2025
Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin

Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin

November 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.