Alal hakika, tarihi ba zai taba mantawa da kisan kiyashi da sojojin mamaya na kasar Japan suka yi a birnin Nanjing na kasar Sin ba. Muggan laifukan yaki da dakarun na Japan suka aikata cikin kwanaki sama da 40 bayan mamaye birnin a ranar 13 ga watan Disamban shekarar 1937 sun yi matukar muni.
Tarihi ya tabbatar da cewa, dakarun na Japan sun hallaka fararen hula Sinawa da dakaru marasa dauke da makamai da yawansu ya haura 300,000, tare da yi wa sama da mata 20,000 fyade. An kuma fayyace wadannan muggan ayyuka cikin kundayen tarihi yadda ya kamata.
To sai dai kuma sabanin abun da ake zato, cewa bangaren Japan zai ci gaba da neman afuwa, da nuna nadamar wadannan abubuwa da suka faru a baya, sai ga shi wasu kafofin watsa labaran kasar na furta wasu kalamai na kokari musanta tarihi.
A wata makala da aka wallafa ranar Litinin din farkon makon nan, editan wata jaridar kasar Japan ya soki wani fim mai suna Dead to Rights, wanda ya yi bitar irin cin zarafin da sojojin Japan suka aikatawa Sinawa fararen hula a wancan lokaci. Har ma dan jaridar ya ce wai batun kisan kiyashi na Nanjing labarin yaudara ne kawai da kasar Sin ta kitsa. Lallai irin wadannan kalamai masu ban mamaki suna da munin gaske, suna kuma dada karfafa zargin da aka dade ana yiwa bangaren Japan na karyata hakikanin tarihi, da nufin sauya gaskiya, da kaucewa daukar alhakin abubuwan da suka faru.
Tun bayan fitar da Dead to Rights a Sin da sauran sassan duniya, fim din ya samu matukar karbuwa, kasancewar ya yi “Waiwaye Adon Tafiya” game da munin ta’asar da dakarun Japan suka aikata a birnin Nanjing a wancan lokaci. To, amma abun tambayar shi ne me ya sa har yanzu wasu masu ra’ayin rikau na Japan ke kokarin kore abubuwan da fim din ya nuna? Amsar wannan tambaya a bayyane take, irin wadannan Japanawa suna tsoron kara bayyanar gaskiya!
Yanzu haka a nan kasar Sin ana ta shirye-shiryen gudanar da babban bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yaki da mamayar sojojin Japan, da nasarar yakin kin tafarkin murdiya, wanda shi ma wani lokaci ne da zai dada tabbatarwa duniya zahirin abubuwan da suka wakana, tare da karyata sassan dake kokarin lullube gaskiya, da kaucewa daukar alhakin ta’asar da aka aikawa al’ummar Sin a yayin mamayar birnin Nanjing.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp